Dan takarar gwamna na jam’iyyar NDC a Jihar Kano kuma tsohon Mataimakin Gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya kalubalanci Gwamnatin Kano da ta gabatar da hujjoji masu inganci kan zargin cewa ya karɓi kuɗaɗen kananan hukumomi ta hannun ɗansa, Mujahid Aminu Abdussalam.
Kalubalen na Gwarzo ya biyo bayan zargin da mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Yusuf, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya yi na cewa an rika tura wasu kuɗaɗen kananan hukumomi zuwa ga tsohon mataimakin gwamnan ta hannun ɗansa.

A wata sanarwa da kakakinsa, Ibrahim Garba Shuaibu, ya fitar a ranar Alhamis, Gwarzo ya bayyana zargin a matsayin mara tushe, yana mai cewa an yi shi ne domin bata masa suna.
Sanarwar ta ce zargin ba shi da wata hujja ko tushe, tare da ƙalubalantar masu zargin da su gabatar da sahihan hujjoji da za su tabbatar da ikirarin nasu.
Kungiyar TTP Ta Musanta Nadin Hon. Nabil Sarki Aliyu A Matsayin Daraktan Matasa
Gwarzo ya kuma jaddada cewa a duk tsawon lokacin da ya yi a harkokin gwamnati ya kasance mai bin ka’idojin gaskiya, riƙon amana da bin doka.
Ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa gaskiya za ta bayyana a ƙarshe, tare da kira ga jama’a da su yi watsi da abin da ya kira zarge-zargen da ba su da tushe ballantana makama.