Shugaba Tinubu ya daga likafar hadiminsa Abdulaziz Abdulaziz

Date:

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙara wa Malam Abdulaziz Abdulaziz girma a aiki, inda ya ɗaga shi zuwa muƙamin Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a (Senior Special Assistant on Media and Public Enlightenment).

Malam Abdulaziz ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafukan sa na soshiyal midiya, inda ya ce ya karɓi takardar tabbatar da sabon naɗin nasa a ranar Laraba.

IMG 20251224 WA0004

Ya ce sabon matsayin sa ya yi daidai da tsarin ayyukan da Shugaban Ƙasa ya amince da su tun ranar 23 ga Afrilu, 2026.

Ya bayyana wannan ƙarin girma a aiki a matsayin wata babbar karramawa da kuma nuna amincewa da gudunmawar da yake bayarwa a aikin sadarwa ta Fadar Shugaban Ƙasa da kuma a fannin yaɗa labarai gaba ɗaya.

‎Majalisar Wakilan Najeriya ta bukaci Tinubu ya inganta tsaro ko ya yi murabus

A cewar sa, sabon matsayin ba wai karramawa ce kawai ba, har ila yau ya ɗora masa sabon nauyi da ƙalubale da ke buƙatar ƙarin jajircewa, ƙwazo da sadaukarwa wajen gudanar da ayyukan sa domin cimma manufofin gwamnati da kuma yi wa ƙasa hidima yadda ya kamata.

Malam Abdul’aziz ya miƙa godiyar sa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa ci gaba da nuna masa amincewa da goyon baya. Haka kuma, ya gode wa shugabannin sa da abokan aikin sa a fannin sadarwa bisa haɗin kai, jagoranci da kuma hangen nesa da suke bayarwa wajen gudanar da ayyukan su.

Ya kuma nuna matuƙar godiyar sa ga abokan aiki, abokan sa da sauran masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai, yana mai cewa gudunmawar da suka bayar ta taka muhimmiyar rawa wajen nasarorin da ya samu a rayuwar sa ta aiki.

Sabon naɗin dai yana daga cikin sauye-sauyen da Shugaba Tinubu yake yi a ɓangaren sadarwa da yaɗa manufofin gwamnatin sa ga jama’a.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sabuwar Takaddama: Gwarzo Ya Kalubalanci Gwamnatin Kano Kan Zargin Cin Hanci

‎ ‎ ‎Dan takarar gwamna na jam’iyyar NDC a Jihar Kano...

‎Majalisar Wakilan Najeriya ta bukaci Tinubu ya inganta tsaro ko ya yi murabus

‎‎ ‎Ɓangaren marasa rinjaye a Majalisar Wakilan Najeriya ta yi...

Sanata Barau Ya Rabawa ’Yan Sandan Kano Ta Arewa Mashina 1,000 Domin Inganta Tsaro

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya sake nuna...

Kungiyar TTP Ta Musanta Nadin Hon. Nabil Sarki Aliyu A Matsayin Daraktan Matasa

Kungiyar Tinubu Transformation Projects (TTP) ta musanta rahotannin da...