Gwamnatin kasar China ta fitar da gargadi mai karfi kan duk wani yunkuri na tsoma baki cikin harkokin cikin gida na Najeriya, bayan kalaman da shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi na barazanar kai hari da sojoji a Najeriya bisa zargin cin zarafin Kiristoci.
Da take jawabi a wajen taron manema labarai a ranar Talata, Mao Ning, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar China, ta bayyana cewa, Beijing “na goyon bayan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu gaba ɗaya yayin da take jagorantar al’ummar Najeriya kan tafarkin ci gaba da ya dace da halin ƙasar.”

“China, a matsayinta na abokiyar haɗin gwiwar Najeriya, tana adawa da duk wata ƙasa da ke amfani da addini ko kare haƙƙin ɗan adam a matsayin hujja don tsoma baki cikin harkokin cikin gida na wata ƙasa ko yin barazanar sanya mata takunkumi ko amfani da ƙarfi,” in ji Mao.
Wadannan kalamai sun biyo bayan martanin ƙasashen duniya kan maganganun Trump da ke haifar da damuwa a diflomasiyya a fadin nahiyar Afirka da ma sauran sassan duniya.