Hedikwatar Tsaron Najeriya ta bayyana cewa babu wata alaƙa tsakanin soke bikin cika shekaru 65 da samun ’yancin kai da kuma zargin yunkurin juyin mulki kamar yadda wasu kafafen labarai suka ruwaito.
A wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaran Hedikwatar Tsaro, Brigediya Janar Tukur Gusau, ya fitar a ranar Asabar, rundunar ta ce labarin da aka yada a kafar yanar gizo batu ne na ƙarya, wanda aka ƙirƙira don tada hankalin jama’a da ɓata sunan rundunar.
Janar Gusau ya bayyana cewa an soke bikin ne domin bai wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu damar halartar muhimmin taron ƙasashen waje, da kuma baiwa dakarun Najeriya damar mai da hankali kan yaƙi da ta’addanci, ’yan bindiga da masu tayar da ƙayar baya.
Ya ƙara da cewa binciken da ake yi kan wasu hafsoshin soja 16 da aka kama ba shi da alaƙa da juyin mulki, illa dai mataki ne na cikin gida da ke da nufin tabbatar da ladabi, bin doka, da ƙwarewa a aikin soja.
Hedikwatar ta roƙi ’yan Najeriya da su yi watsi da labaran ƙarya, tana mai tabbatar da cewa rundunar sojin ƙasar na da cikakken biyayya ga kundin tsarin mulki da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tare da nuna ƙudurinta na tabbatar da dorewar demokiradiyya a Najeriya.