Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke hukunci a kan wasu mutane shida da aka samu da laifin gurbata muhalli, bayan sun zubar da shara da kuma kayan gini a kan titi a yankin Sabon Gari.
Mai gabatar da kara, Barista Bahijja H. Aliyu, ta ce wadanda ake tuhuma sun aikata laifin da ya sabawa dokar tsaftar muhalli ta jihar, bayan sun ki bin umarnin hukumar tsafta da ta gargade su tun farko.
Lauyan ta ce hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar Kano, karkashin jagorancin Dr. Muhammad S. Khalil, ta aika musu da takardar gargadi, tana umartar su su kwashe kayan ginin da suka zubar da kuma su tsabtace wuraren kasuwancinsu, amma suka yi biris da umarnin.
Da aka karanta musu tuhumar a gaban alkalin kotun, Halima Wali, dukkaninsu sun amsa laifinsu.
Kotun ta yanke musu hukuncin daurin sati biyu a gidan gyaran hali ko kuma biyan tarar naira dubu dari biyu (₦200,000) kowannensu.
Laifukan da aka samu su da su sun haɗa da rashin tsaftar kofar shaguna, rashin samar da kwandon shara, zubar da shara a magudanan ruwa, da kuma zubar da yashi, dutse da bulo a kan titi — musamman a yankin France Road, Sabon Gari, Kano.