Majalisar shura ta jihar Kano ta gaiyaci Sheikh Lawan Abubakar Triumph bisa ƙorafe-ƙorafe da aka miƙa mata na zargin furta kalaman ɓatanci ga Ma’aiki Annabi Muhammad (SAW).
Haka zalika majalisar ta gaiyaci waɗanda suka mika ƙorafe-ƙorafen domin zama a ji ta bakin ki wanne ɓangare.
Da ya ke zantawa da manema labarai bayan zaman majalisar na farko tun da aka kafa ta, Sakataren majalisar kuma Kwamishinan Kasuwanci, Shehu Wada Sagagi ya tabbatar da cewa an mikawa majalisar ƙorafe-ƙorafe har guda 8 daga kungiyoyin addini da na al’umma.
Ya ce majalisar ta duba ƙorafe-ƙorafen kuma za ta gayyaci kowanne ɓangare, har da shi ma Malam Triumph din don jin ta bakin sa.
Haka zalika Sagagi ya kara da cewa Majalisar za ta yi aiki tsakani da Allah don baiwa gwamnati shawarar da ta dace.