Allah ya yiwa Sarkin Gabas kuma Hakimin Kabo Alhaji Idris Adamu Dankabo Rasuwa

Date:

 

Inna lillahi wa’inna ilaihirrajun

Allah ya yiwa Sarkin Gabas kuma Hakimin Kabo Alhaji Idris Adamu Dankabo Rasuwa.

Alhaji Idris Adamu Dankabo ya rasu, ya na da shekaru 48.

Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayi Alhaji Idris ɗa  ga marigayi Jarman Kano, Alhaji Muhammad Adamu Dankabo, ya rasu ne sakamakon haɗarin mota da yayi a cikin Birnin Kano.

Ya rasu ya bar mata ɗaya da ƴaƴa biyu.

Nasarar da Ɗaliban Kano suka Samu a NECO Kokari ne na Gwamnatin Ganduje – Sanusi Kiru

Za a yi jana’izar sa a yau Juma’a da misalin ƙarfe 10 na safe a fadar Sarkin Kano, Kofar Kudu, inda ake sa ran Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ne zai yi masa sallah.

Allah Ya gafarta masa, Ya sa aljanna ce makomar sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar ODPMNigeria ta shirya taron tattaunawa da matasa a Bichi

Daga Ahmad Isa Getso   Ƙungiyar Rajin Kawo Sauyi da Cigaba...

Yadda Dansanda ya harbe kansa da bindiga a Kano

Wani jami’in dansanda mai suna Aminu Ibrahim ya rasa...

Hukumar jin daɗin alhazai ta Kano ta sanar da kuɗin aikin hajjin badi

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta amince...

Kudade: Ganduje ya caccaki Gwamnatin kano

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Tsohon shugaban jam’iyyar APC...