Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Bichi kuma shugaban Kwamitin kasafin Kudi na majalisar Hon. Abubakar Kabir Bichi, ya raba sabbin motocin bas masu daukar mutane 16 ga jami’o’i da kwalejojin ilimi a Kano da taraktoci guda 11 don inganta noma da Ilimi a Kano .
Kadaura24 ta rawaito wakilai daga jami’o’i da manyan Makarantu daban-daban na jihar Kano sun halarci taron rabon kayayyakin, wanda aka gudanar a ranar Litinin a garin Bichi.

Hon. Abubakar Kabir Abubakar Bichi ya samu wakilcin shugaban kwamitin ilimi Dakta Habibu Usman Abdu da manyan hadimansa na majalisa Sabo Ilyasu Saye da Zahraddeen Kabir da sauransu .
Manyan makarantun da suka ci gajiyar shirin sun hada da Jami’ar Bayero (BUK), wacce ta samu motocin bas 2, jami’ar Northwest ta Kano motocin bas guda biyu, Jami’ar Aliko Dangote dake Wudil motocin bas guda biyu, FCE Bichi bas guda biyu, Jami’ar Tarayya ta Yusuf Maitama Sule take Kano bas daya, Ibrahim Ayagi College of Health Science Dawakin Tofa, Aminu Kano College of Islamic Legal bas daya, Aminu Kano College of Islamic and Legal studies bas, Sa’adatu Rimi college of Education bas daya.
An kuma raba taraktoci goma sha daya da injinan gurbi na zamani guda 4 ga mazabun goma sha daya dake fadin karamar hukumar Bichi.
Hon. Abubakar Kabir Abubakar Bichi ya ce ya bayar da motocin ne ga manyan makarantu da nufin saukaka kalubalen sufuri a makarantun .
Ya kara da cewa taraktoci goma sha daya da injinan girbin da aka raba ya bayar da su ne don inganta harkokin noma a mazabu goma sha daya da ke karamar hukumar Bichi.
Yayin taron an zayyano wasu daga cikin aiyuka da Hon. Abubakar Kabir Bichi ya yi na tallafawa fannin ilimi .
Irin wadannan ayyukan tallafi da Hon. Abba Bichi ya ke yi a fannin ilimi da dai sauran su ne suka sa Jami’ar Tarayya, Kashere dake Jihar Gombe da Jami’ar Tarayya ta Dutsin-ma dake jihar Katsina suka baiwa Abubakar Kabir Bichi digirin girmamawa.