Kungiyar Direbobin Tashar Malam Kato ta Mika ta’aziyyar rasuwar Aminu Dantata

Date:

Daga Ibrahim Sani Gama

 

Kungiyar matuka motocin haya dake tashar malam kato, (bus 9) ta Mika sako ta’aziyyarta ga Gwamnatin jihar Kano da masarautar Kano da kuma iyalan murigayi Alhaji Aminu Alhasan Dantata da sauran al’ummar jihar Kano, bisa rasuwa murigayi Allah Aminu Alhasan Dantata daya rasu ya na da shekaru 94 .

Mataimakin kungiyar Alh. Samaila sale giredi ne ya bayyana haka a yayin wata tattarawa da yayi tare da manema labarai a ofishinsa .

Ya ce rasuwar Alhaji Aminu Alhasan Dantata,ba karamin rashi ba ne ga al’ummar jihar Kano da ma kasa baki daya.

InShot 20250309 102512486
Talla

Samaila giredi ya bayyana cewar, a madadin ‘yankungiyarsa ta NURTW dake tashar malam kato, suna baiwa iyalan murigayin da kungiyoyi na yankasuwa da sauran al’ummar jihar Kano taaziyya bisa wannan gagarumin Rashi da aka Yi Wanda ba za”a taba mantawa da shi ba.

Samaila sale yace Alh Aminu Alhasan Dantata ya taimakawa al’ummar jihar Kano, musamman yankasuwa da suke kokarin durkushewa bisa karayar Arziki da dai daikun mutane Wanda ba’a iya kirga su ba.

Samaila giredi yace, murigayin ya cibiyoyi da kamfanoni domin taimakawa alummar jihar Kano da sana’oin da za su dogara da kansu.

Dangane da masallatai da gidajen zama ya Gina ya bayar a matsayin sadakatul jariya,idon aka koma fannin harkokin ciyarwa Nan ma ba za’a manta da shi ba .

Alhaji samaila sale yayi Kira ga sauran masu hannu da shuni da su Yi koyi da hayan murigayi Allh Aminu Alhasan Dantata ta yin karamci ga sauran alummar jihar Kano da Kuma, makamantan abubuwa a kasashen ketare, Inda Kuma, yayi fatan Allah subahaanahu wata”ala ya jikansa da Rahman da iyayensu tare da sauran alummar Duniya baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...