NigArmy@162: Rundunar Sojin Nigeria ta yi gangamin kula da lafiyar al’umma kyauta

Date:

Daga Abdulrazak Kauran Namoda

 

Hedikwatar runduna ta 1 ta sojojin Najeriya dake Gusau, ta gudanar da wani gangamin Kula da lafiyar al’ummar garin Rawayya dake karamar hukumar Bungudu a jihar Zamfara, kyauta a wani bangare na bikin murnar zagayowar ranar kafuwar Rundunar sojojin Najeriya ta shekarar 2025 (NADCEL).

Birgediya Janar Timothy Opurum, Kwamandan Birgediya ne ya jagoranci shirin bayar da agajin da nufin inganta hulda tsakanin fararen hula da sojoji da kuma nuna jajircewar Sojoji wajen kula da lafiya da jin dadin al’ummar yankin.

InShot 20250309 102512486
Talla

A yayin taron wanda aka gudanar a Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Rawayya, an baiwa marasa lafiya shawarwari, magunguna, da masu ciwon ido, masu hawan jinin jini, da sauransu kyauta ga daruruwan mazauna garin da suka hada da mata da tsofaffi.

“Ba yaki ko fada da yan taa’adda kadai muke ba , Muna yin aiyukan taimakon irin wadannan don inganta hulɗa tsakaninmu da mutanenmu,” in ji Brig Gen Opurum.

Yanzu:yanzu: Gwamnan kano ya yi sabbin nade-naden mukamai

Ya ce shirin ya yi dai-dai da manyan manufofin hadin gwiwa na rundunar soji da farar hula, wanda aka yi shi domin murnar cikar Rundunar sojin Nigeria shekaru 162 da kafuwar.

Hakimin Rawayya, Alhaji Abubakar Rashi, da wasu da suka amfana da Shirin sun yabawa Rundunar bisa Wannan kokari da ta wanda suka ce shi ne irinsa na farko da suka fara gani.

“Muna matukar godiya ga Sojoji. Wannan babban abin alfahari ne da ba za mu taba mantawa da shi ba,” in ji shi, yana mai addu’a ga rundunar ta ci gaba da samun nasara wajen magance matsalar rashin tsaro a Nigeria .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...

Tinubu ka fadawa yan Nigeria Inda ka tsaya har kwana 5 bayan taron BRICS – ADC

    Jam'iyyar African Democratic Congress wato ADC ta soki Shugaban...

Da dumi-dumi: Yadda akai Jami’an tsaro suka kama ni -Danbello

Rahotannin sun tabbatar da cewa jami'an tsaro a Nigeria...