Ni da kaina na je ofishin EFCC – Ajiya

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Tsohon Babban Jami’in Kudi (CFO) na Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), Umar Ajiya Isa, ya karyata rahotannin da ke cewa jami’an Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) sun kama shi a ranar Litinin bisa zargin almundahana.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ajiya ya bayyana cewa, akasin yadda ake yadawa, shi da kansa ne ya je ofishin EFCC domin amsa tambayoyi, ba tare da an kama shi ba dangane da zargin handame cinikin man fetur har ma dala biliyan $7.2 a matatun mai na Warri da Port Harcourt.

InShot 20250309 102512486
Talla

“Ba wanda ya kama ni kan zargin batan wata dala biliyan $7.2 a matatar mai. Na je ofishin EFCC ne da kaina domin amsa tambayoyi sannan na koma gida. Na ji takaici ganin rahotanni a kafafen yada labarai da ke cewa an kama ni bisa zargin damfara,” in ji shi.

“Na yi aiki a NNPC Limited kuma na baro wurin da mutuncina kuma na yi aiki na cikin tsabta. Babu wanda ya taba zargina da wani nau’in damfara duka tsawon lokacin da na yi a kamfanin. Wadanda ke yada wannan ƙarya suna so ne kawai su bata mini suna.”

Iyalan mafarautan da aka kashe a Edo sun zargi gwamnatin kano da yin watsi da su

Isa ya ce a shirye ya ke a kowane lokaci ya kare mutuncinsa da shekaru da ya kwashe yana aiki a NNPCL.

“Ina nan cikin ƙasar nan kuma a duk lokacin da EFCC ta bukaci na bayyana a gaban ta, zan je ba tare da wata matsala ba,” in ki Ajiya.

A makon da ya gabata ne dai Kwamitin Majalisar Dattawa kan Kuɗaɗen Al’umma karkashin jagorancin Sanata Aliyu Wadada, ya bayyana cewa akwai zargin sama-da-faɗi da wasu Kuɗaɗe da suka kai tiriliyoyin Naira a cikin bayanan kudi da aka tantance na NNPCL.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Kwamitin ya bayyana hakan a matsayin abin damuwa da takaici.

Kwamitin ya ce damuwar na da nasaba ne da bayanan kudi na NNPCL da aka tantance daga shekarar 2017 zuwa 2023.

Nan take kwamitin ya mika jerin tambayoyi 11 ga sashen kudi na NNPCL tare da ba su mako guda su dawo da amsoshi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Inganta tsaro: Shugaban K/H Tarauni ya ba da fili domin gina ofishin Civil Defence a karkasara

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Shugaban karamar hukumar Tarauni, Alhaji Ahmed...

Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-nade

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nada Malam...

Gwamnatin Kano ta bada hutun sabuwar shekarar Musulunci

Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana gobe Alhamis, 26 ga...

Rundunar tsaron dazuka ta nemi hadin kan gwamnatin Kano don yakar fadan daba

Daga Ibrahim Sani Gama   Rundunar jami'an tsaro dake kula da...