Gwamna Abba ya ba da Umarnin gyara makarantar koyon harsunan Faransanci da Chananci dake Kano

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusif, ya ba da umarnin a gaggauta gyara makarantar koyon harsunan Faransanci da Sinanci mallakar gwamnatin jihar, a ƙoƙarinsa na bunƙasa ɓangaren ilimi da inganta koyo da koyarwa a jihar Kano

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.

Sanarwar ta ce umarnin gwamnan ya biyo bayan wata ziyarar bazata da ya kai makarantar da ke garin Kwankwaso, a ƙaramar hukumar Madobi a farkon makon nan.

InShot 20250309 102512486
Talla

A cewar Gwamnan, “Na kai ziyara makarantar ne domin na ganewa idanuna yadda ɗalibai da malamai ke gudanar da harkokinsu, da kuma yanayin gine-ginen makarantar”.

Gwamnan ya bayyana jin daɗinsa bisa ƙwazon malamai da ɗaliban, musamman yadda ɗaliban ke iya magana da kyau da harsunan Faransanci da Sinanci.

Iyalan mafarautan da aka kashe a Edo sun zargi gwamnatin kano da yin watsi da su

“Za mu gyara makarantar ba tare da ɓata lokaci ba, adon haka na umarci Kwamishinan aiyuka da ya hanzarta fara aikin gyaran gine-ginen da suka lalace a makarantar”.

sanarwar ta ce wannan mataki na daga cikin tsare-tsaren gwamnatin Kano, na inganta ilimi da samar da ingantacciyar nagarta a fannin koyon harsuna domin bunƙasa ci gaban jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Inganta tsaro: Shugaban K/H Tarauni ya ba da fili domin gina ofishin Civil Defence a karkasara

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Shugaban karamar hukumar Tarauni, Alhaji Ahmed...

Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-nade

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nada Malam...

Gwamnatin Kano ta bada hutun sabuwar shekarar Musulunci

Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana gobe Alhamis, 26 ga...

Ni da kaina na je ofishin EFCC – Ajiya

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon Babban Jami’in Kudi (CFO) na...