Ciyaman din Wudil ya kaddamar da aikin gina magudanan ruwa a wasu garuruwa a yankin

Date:

Daga Maryam Adamu Mustapha

 

Shugaban karamar hukumar Wudil, Hon. Abba Muhammad Tukur, ya kaddamar da aikin gina magudanan ruwa, da gina kwalbati don magance faruwar Ambaliyar ruwa a garin Katurje, dake mazabar Dagumawa a yankin.

Wannan gagarumin aikin ya taso ne daga gidan Amadu Jagwab zuwa Coko Club a Katurje. Inda aikin zai hadar da gina manyan kwalbatoci guda biyu da gina magudanan ruwa a gefe da gefe, wanda aka za a yi don dakile ci gaba da ambaliyar ruwa da ta dade tana shafar mazauna garin Katurje da makwabtansu.

InShot 20250309 102512486
Talla

Shekaru da yawa, da dama al’ummar yanki suna shan wahala sosai musamman a lokacin damina wanda ke haifar da yawaitar ambaliyar ruwa, zaizayar ƙasa, da lalata gidaje da kadarori a duk shekara.

Yanzu-yanzu: Kotu ta yi kwarya-kwaryar hukunci akan zargin rashawa da ake yiwa Ganduje da mai dakinsa

A wata sanarwa da Babban sakataren yada labaran shugaban karamar humar Nura Mu’azu Wudil ya aikowa Kadaura24, ya ce Wannan aikin ya sake nuna kwazo Hon. Tukur wajen samar da ababen more rayuwa, da inganta yankunan karkara, da kuma kare lafiyar al’umma a fadin karamar hukumar Wudil.

Yayin da yake jawabi Hon. Abba Muhammad Tukur ya jaddada mahimmancin aikin wajen dakile ambaliyar ruwa da inganta hanyoyin sufuri, don saukakawa manoma da ’yan kasuwa wajen gudanar da harkokinsa don kyautata rayuwarsu al’ummar yankin.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Ya kuma tabbatar wa da al’ummar Katurje da kewaye cewa gwamnatin sa na ci gaba da jajircewa wajen ganin an samu ci gaba daga tushe da kuma samar da hanyoyin da za su dace da jama’a wadanda kuma za su inganta rayuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

“BAMA YI”: Kalma mai alamta tsayuwar alkiyamar raggo ko mutakabirin dansiyasa – Dr. Murtala Iliyasu Ayagi

  Daga Dr. Murtala Iliyasu Ayagi malamin a Kwalejin Koyar...

2027: Tinubu ya bayyana lokacin da zai ambata sunan wanda zai yi masa mataimaki

I'mFadar Shugaban Kasa ta ce shugaba Bola Tinubu zai...

Abba Gida-gida ya karrama yan kasuwar Singa yayin dawowarsa Kano bayan kammala aikin Hajji – Liti Kwasangwami

Daga Ibrahim Sani Gama   Kungiyar kwankwasiyya singa market dake jihar...