Wata tawaga dake rajin aikin da Dimokaradiyya a Nigeria (Nigeria Democracy Working Team) ta bukaci al’ummar jihar Kano da su yi watsi da wasu maganganu da tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji ya yi a karkashin wata kungiya a jam’iyyar APC, inda ya zargi gwamnatin jihar Kano da rashin kyakkyawan alkiblar da nuna Wariya da ganawa wajen tafiyar da al’amuran jihar.
Idan za a iya tunawa a wata bita Shekaru Biyu da ya yi wa gwamnatin NNPP a jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji, ya yi kakkausar suka ga gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf, inda ya zarge ta da rashin iya gudanar da mulki da kuma rashin tabuka komai.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban Tawagar kungiyar Nigeria Democracy Working Team Muhammad Salis ya sanyawa hannu kuma aka aikowa Kadaura24.
“Dole a yi watsi da wadancan zarge-zargen na Alhaji Usman Alhaji saboda akwai son rai da rashin hujjoji a cikinsu. Dama me kake tsammani ga dan Siyasa irin Usman Alhaji wanda ba shi da goyon bayan kowa saboda yadda ya rika shan kaye a zabukan da ya tsaya a baya, da kuma rashin samun nasara ga duk wanda ya goyawa baya”.
Wadannan kalaman da Usman Alhaji ya ke yi kawai yana yin su ne saboda neman suna kuma ya ga ba shi da wani katabus a da’irar Siyasar jihar Kano shi yasa yake ta surutai barkai.
Zargin Abba gida-gida ba ya aiki a Kano : Tijjani Sarki ya caccaki Usman Alhaji
Hanya daya wadda ta fi dacewa a kwatanta halin da yake ciki ita ce karin maganar na ta Hausawa da ke cewa “Tururuwa a cikin taso rayuwar fukafuki ta kan yi”.
Ko da yake Alhaji Usman Alhaji ya rike manyan mukamai a siyasa, ya taba zama babban Sakataren jam’iyyar NRC, Ya kuma rike mukamin kwamishinan ilimi a jihar Kano, daga baya kuma ya zama sakataren gwamnatin jihar, amma duk da haka ta tabbata duk wadannan mukamai da ya rike ba wai an ba shi su ba ne don ya chanchanta. Ya tsaya takarar a lokuta daban-daban Amma bai taba yin nasara ba, shi yasa muke ganin yana wadancan kalamai ne don kawai ya nemi sunan don a kirawo shi a ba shi Mukami.
Idan aka yi nazarin rayuwar Alhaji Usman Alhaji na kut-da-kut, za a fahimci yadda a kullum yake fuskantar koma-baya a harkokin siyasa, kuma dama tuni tauraruwarsa ta disashe a harkokin siyasa.
Ta yaya dan siyasar da ya rike muhimman mukamai a jam’iyyun siyasa a matakin kasa da jiha zai, Amma saboda komawa baya ya zo ya rika shugabantar wata kungiya a jam’iyya? .
A shekarar 2007, Alhaji Usman Alhaji ya tsaya takarar Sanata a karkashin jam’iyyar PDP, amma ya sha kaye a hannun Sanata Kabiru Ibrahim Gaya.
Haka dai ya sake tsayawa takarar majalisar dattawa a karkashin jam’iyyar CPC a shekarar 2011, haka ya sake Shan kaye ya fadi zabe.
Zargin cin Bashi: Gwamna Abba bai taba ciyo bashi ba – Gwamnatin Kano
A zaben 2015, ya kasance daya daga cikin wadanda suka fito fili a kafafen yada labarai yana neman takarar gwamnan Kano, amma mutane sun kasa gane yadda akai ya janyewa Dr. Abdullahi Umar Ganduje wanda shi ma yana cikin masu neman takarar, amma daga bisani Ganduje ya biya shi diyya ta hanyar ba shi mukamin Sakataren gwamnatin jihar Kano .
Masana ilimin halayyar dan adam sun ce duk mutumin da ya sha kaye a zabuka daban-daban to akwai yiwuwar ya Sami matsala a kwakwalwarsa ko ma gangar jikinsa.
Wannan fa mutum ne da ya samu damar rike mukamai masu muhimmanci a fagen ilimi, daga baya kuma ya rike a fagen siyasa, amma abun takaici yanzu ya zo ya damu kansa dole sai ya shugabanci wata kungiyar bogi.
Duk da kalaman mutane irin su Alhaji Usman Alhaji ba za mu manta da irin aiyukan Alkhairin da Gwamnatin NNPP, karkashin Alhaji Abba Kabir Yusuf ke ba musamman a bangarorin da suka shafi harkokin ilimi, bunkasa kiwon lafiya, noma da dai sauransu.
A bayyana yake yadda al’ummar jihar Kano suke cikin farin da salon jagorancin mai girma Gwamna, Alhaji Abba Kabir Yusuf.