Zargin Abba gida-gida ba ya aiki a Kano : Tijjani Sarki ya caccaki Usman Alhaji

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Babban sakataren ba kungiyar Eye On Kano Initiative Tijjani Sarki ya bukaci al’ummar jihar Kano da su yi watsi da Kalaman tsohon Sakataren gwamnatin Kano Alhaji Usman Alhaji na cewa gwamnan kano Abba Kabir Yusuf ya Kasa tabuka wani abun a zo a gani a Kano.

” Wannan zargi ne maras tushe ballantana makama, rashin abun fada ne ya sa Usman Alhaji ya fito yana wadannan kalaman, kawai saboda ya je ya kwashi AC ya rasa abun fada shi yasa ya fito yana zantuttuka ba hujja”.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Tijjini Sarki ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24, a matsayin martani ga Kalaman da tsohon sakataren gwamnatin Kano Alhaji Usman Alhaji ya yi a wasu kafafen yada labarai a Kano.

Ya ce Babu shakka gwamnatin jam’iyyar NNPP dake karkashin gwamna Abba Kabir Yusuf ta chanchanci a yaba mata saboda yadda ta mayar da hankali wajen gudanar da aiyukan raya kasa da cigaban al’umma a lungu da Sako na jihar Kano.

Zargin cin Bashi: Gwamna Abba bai taba ciyo bashi ba – Gwamnatin Kano

” Bai kamata ace wani Dan APC a Kano ta fito yana irin wadannan maganganu ba, kamata yayin su rika boye kawunansu su daina shiga cikin al’umma saboda kunyar rashin tabuka komai lokacin suna gwamnati a Kano, ban da cutar da Kano da mutanen Kano ba abun da suka yi”.

Bari mu yi duba Kan wasu aiyuka daki-daki:

1 – A bangaren Samar da ruwan Sha a Kano , a baya kowa yasa mawuyacin halin da Kano ta sami kanta saboda rashin Ruwa, Amma yanzu kowa ya shaida kokarin da Gwamna Abba ya ke yi don gyara matsalolin da APC ta haifar a bangaren Ruwa a Kano .

2- Bangaren Ilimi : Gwamnatin APC ta lalata ilimi ta hanyar kin gyaran Makarantu , rashin Samar da ƙwararru Malamai da danne hakkokin Malamai da sauransu.

Sabanin hakan yanzu gwamnatin NNPP ta himmatu wajen gyara wadancan matsalolin ta hanyar Samarwa da gyara Makarantu, Samar da ƙwararrun Malamai da kuma biyansu hakkokinsu akan kari da dai sauransu.

3- Gwamnatin APC ta yanka tare da sayar da filayen Makarantu, Asibitoci, Makabartu da dai sauransu.

Tabbas da Abba ya zo ya yi rusau, Amma irin wadancan wurare ya rushe saboda ba yanka su akan tsari ba, sai dai son zuciya da rashin kishin Kano , hakan ta sa Gwamnatin NNPP ta rushe su.

InShot 20250309 102403344

4- Maganar Samar da wutar lantarki Mai zaman kanta ta jihar Kano ba Gwamnatin APC ce ta fara ba kawai ta gaji aikin ne , kuma har ta tafi ba ta kammala aikin kamar yadda aka tsara shi ba.

5- Batun fadin albarkacin baki gwamnatin Abba Kabir Yusuf tana kokari Sosai wajen jure duk Kalaman da yan adawa suke amfani da su wajen kalubalantar gwamnatin duk da cewa a wasu lokuntan yan adawar suna wuce gona da iri.

Tun da Abba ya sama Gwamna Bai taba samun matsala da wata kafar yada labarai ko wani Dan Jarida ba, sai dai mai kokarin inganta alakar aiki a tsakaninsu.

Alkaluma sun nuna cewa daga watan Janairu zuwa wata fabarairu na Wannan Shekarar ta 2025 an karya ka’idojin hukumar Kula da kafafen yada labarai akalla sau 262, Amma ba ko guda da gwamnatin Kano ta dauki mataki akai duk da cewa gwamnatin aka ci zafi.

Akwai sauran aiyuka da dama da gwamnatin Abba ta yi wanda gwamnatin APC ta Kasa yi a bangarori daban-daban.

“Ina sanar da Usman Alhaji da yan barandansa su Sani gwamnatin NNPP karkashin Abba Kabir Yusuf ta himmatu wajen Samar da aiyukan raya kasa da cigaban al’umma sabanin gwamnatinsu da ta gabata wacce ta Mai da hankali wajen azurta wasu mutane kalilan”.

Tijjini Sarki ya ce “Ina kira ga yan jam’iyyar APC da su saurarawa Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf su bar shi ya cigaba da yiwa al’ummar jihar Kano aiyukan alkhairi don ya ciyar da jihar gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...