Daga Ibrahim Sani Gama
Shugaban kungiyar kwankwasiyya na kasuwar Singa Alhaji Liti Kwasangwami ya shawarci al’ummar kasuwar da su yi watsi da wata sanarwa da wata kungiya a kasuwar ta fitar na cewar yan kasuwar kar su fito domin yin kasuwancinsu ranar lahadi saboda sun shirya yin gangamin sharar kasuwar.
Alhaji Liti kwasamgwami ya sanar da haka ne a lokacin da ya ke zantawa da Kadaura24 a ofishinsa.

Liti kwasamgwami ya ce wannan sanarwar da suka fitar bata da tushe ballantana makama, a don haka yake sanar da al’ummar kasuwar ta singa da su fito domin gudanar kasuwancinsu kamar yadda su ka saba a kodayaushe.
Shugaban kungiyar ya kuma yabawa Gwamnan jihar Kano injiniya Abba Kabir Yusuf bisa yadda ya yi kokari domin ganin Mahajjatan Kano sun gudanar da aikin hajjinsu lafiya.
Ya ce gwamnan jihar Kano injiniya Abba Kabir Yusuf ya taka mahimmiyar rawa ta fannin taimakawa alhazan jihar Kano da tallafin kudade da samar musu da ingantaccen matsuguni yayin gudanar da ibadarsu wanda kuma suka yi ta cikin kwanciyar hankali da lumana.
Shugaban kungiyar Alhaji kwasamgwami ya yi kira ga Gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf daya waiwayi kungiyar kwankwasiyya singa market bisa gudunmawar da take baiwa ci gaban gwamnatinsa musamma yadda wasu mutane su ke ganin kamar sun tura mota ta bulesu da hayaki.
Daga karshe shugaban kungiyar Alh liti kwasamgwami ya ce tunawa da kungiyar zai taimakawa kungiyar wajen fita daga cikin kalubalen yan adawa dake kokarin sare mata gwiwa da gatari.