Tsohon Dan takarar shugaban karamar hukumar Gwarzo Alhaji Kabiru D Bello ya yabawa mataimakin Gwamnan jihar Kano Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo bisa yadda ya taimakawa mutane da yawa domin sauke farali a bana .
” Tabbas abun alkhairin da mataimakin gwamnan ya yi min ba abun da zan ce sai godiya, ya taimake ni na sauke farali a Wannan Shekarar, don haka ya yi min abun da ba wanda ya taba yi min a rayuwata”.

Alhaji. Kabiru D Bello ya bayyana hakan ne a wata zantawa da ya yi da wakilin Kadaura24 a birnin Makka.
Gidajen Wasanni a Kano sun bi ka’dojin da muka sanya musu yayin bikin sallah – Abba El-Mustapah
” Ranar da mataimakin gwamnan ya sanar da ni cewa ya saka ni cikin wadanda za su je kasar Saudiyya domin yin aikina na Kula da lafiya kuma in sauke farali, a ranar kwata-kwata na Kasa samun nutsuwa kuma ban yi bacci ba saboda farin ciki”. Inji Kabiru Bello
Alhaji Kabiru D Bello ya ce mataimakin gwamnan yana tallafawa matasa sosai domin inganta rayuwarsu don su dogara da kawunansu.
” Ina kuma godewa mai gayya mai aiki balaraben gwamnan Kanawa, Alhaji Abba Kabir Yusuf , saboda yadda yake gudanar da aiyukan cigaba domin bunkasa jihar Kano”.
Ya yi Addu’ar Allah ya sakawa mataimakin Gwamnan da mafificin alkhairi ya sake daga darajarsa domin ya cigaba da taimakawa rayuwar al’umma.