Gidajen Wasanni a Kano sun bi ka’idojin da muka sanya musu yayin bikin sallah – Abba El-Mustapah

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

A wani bangare na kokarin tabbatar da tsafta da kuma da’a yayin bukukuwan Sallah Babba a jihar Kano, Hukumar Tace Fina-Finai da Dab’i ta Jihar Kano karkashin jagorancin Shugaban Hukumar Abba El-Mustapha, ta bayyana jin dadinta bisa yadda Dakunan Taro da gidajen wasannin a Kano suke bin dokokin ta a yayin Bikin Babbar Sallah.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Kwamitin da ke da alhakin sa ido kan ayyukan wadannan guraren taro a lokacin Sallah ne ya tabbatar cewa dukkannin guraren da suka sami damar kai ziyara sun cika ka’idojin da hukumar ta shimfida a yayin bukukkuwan sallar. Wannan bayani ya fito ne daga Shugaban Kwamitin, Alh. Lawan Hamisu Danhassan, wanda shi ne Daraktan dake lura da sashin Fina-Finai da Cigabansa a Hukumar.

Matsalar Ruwan: Shugaban K/H Wudil ya ba da Umarnin gyara rijiyoyin burtsatse 100 a yankin

Ya bayyana cewa hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an ci gaba da bin doka da oda, tare da daukar matakin da ya dace kan duk wanda ya karya doka batare da sani ko sabo ba. Ya kuma bukaci masu dakunan taro da gidajen wasanni a Jahar Kano da su cigaba da bada hadin kai domin tabbatar da kiyaye al’ada tare da tarbiyar addinin musulunci.

InShot 20250309 102403344

Danhassan ya bayyana godiyarsa ga Shugaban Hukumar Abba El-mustapha bisa yarda da kafa kwamitin tare da dora masa alhakin sa ido tare da tabbatar da da’a a tsakanin masu zuwa gidajen wasannin tare da dakunan taron dake Jahar Kano. Ya kuma yaba wa Gwamnatin Jihar Kano bisa goyon bayanta ga aiyukan hukumar tare da amsa bukatun Hukumar akan lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...

Sojoji sun mikawa Tinubu Shawarwari yadda za a kawo karshen matsalar tsaron Nigeria

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan...

Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da nadin...

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Koma Jam’iyyar APC a Hukumance

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar...