Hamza Ibrahim Baba Shugaban hukumar kula da shirin gwamnatin tarayya na tallafawa kananan noma da yan kasuwa Maza da mata don inganta sana’o’insu (GEEP) ya sha alwashin bunkasa rayuwar matasa masu tarin yawa a Nigeria don tabbatar da manufar samar da shirin.
“Shirin GEEP ya kunshi tallafawa kananan manoma da kananan yan kasuwa domin a tallafa musu a daga darajar sana’o’in da suke yi, ta hanyar ba su ko kara musu jari don ya zamana sun bunkasa sana’o’in nasu don inganta tattalin arzikin Nigeria”.

Alhaji. Hamza Ibrahim Baba Dawakin Tofa ya bayyana hakan ne yayin taron taya shi murnar mukamin da shugaban Kasa ya bashi na shugabantar hukumar GEEP, wanda abokansa suka shirya masa a Kano.
Ya ce zai yi amfani da Wannan damar wajen inganta sana’o’in Matasa masu tarin yawa saboda Matasa su ne kashin bayan cigaban Kowacce al’umma .
Rikici: Dan Majalisar NNPP ya zargi Sanusi Bature da yi wa Gwamnan Kano zagon kasa
Baba ya kuma yi alkawarin hada Kai da hukumomi daban-daban a Nigeria da ma Kungiyoyin kasashe waje domin cimma manufar da Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya dora masa.
” A baya na Sami dama kuma na taimakawa mutanenmu na karamar hukumar Dawakin Tofa , Amma yanzu zan fadada taimakon zuwa ga duk matasan Kasar nan dake fadin kananan hukumomin kasar nan, saboda Wannan Shirin na Kasa ne baki daya”. Inji Hamza Baba
Hamza Baba ya godewa dukkanin mahalarta taron musamman abokansa na karamar hukumar Dawakin Tofa da suka tsaya tsayin daka don ganin sun shirya masa taron karramawar ba tare da sun nemi ko da sisin kobo a hannunsa ba.
” Ina mika godiya iyayena da yaye na da abokaina da muka hadu a nan don ku taya ni murna , Ina kuma neman addu’o’inku saboda aiki ne Babba aka dora min , kuma na kudiri aniyar yin Gaskiya da rikon amana har sai mun taimakawa masu karamin karfi a Kasar nan”.
Al’umma da dama ne suka halarci taron da ko’ina a fadin jihar Kano, daga cikinsu har da wakilcin shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano da Shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar Kano da Kasa baki daya.