Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Dan majalisar wakilai Mai wakiltar kananan hukumomin Dawakin Tofa, Tofa da Rimin Gado Engr. Tijjani Abdulkadir Jobe ya zargi mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa da yi wa gwamna da yan jam’iyyar NNPP zagon kasa a yankin da ya fito.
Cikin wani fefen bidiyo da Kadaura24 ta kalli, mun hangi Jobe yana wata ganawa da magoya bayansa, inda yake bayyana Daraktan yada labaran Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, a matsayin mai yiwa Jam’iyya zagon kasa, ta hanyar hada kai da dan gidan tsohon Gwamnan Kano, Umar Abdullahi Umar (Abba Ganduje).

Jobe yace lallai ya kamata Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya dauki mataki akan Sanusi Bature, domin baya wakiltarsa kuma baya wakiltar jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Kwankwaso Ya Karbi Magoya Bayan Kawu Sumaila sama da 1,200 da su ka koma NNPP
” Ina kira ga Mai girma gwamnan da ka ja kunne mai magana da yawunka Sanusi Bature Dawakin Tofa saboda yana hada Kai da ya’yan Ganduje da gwaggo wajen kawo Rikici a jam’iyyarmu ta NNPP musamman a yankin mu na kananan hukumomin Dawakin Tofa, Tofa da Rimin Gado”. Inji
A baya bayan nan dai, an ga yadda magoya baya ke dafifi a Gidan Sanusi Bature, domin yi masa fatan alheri akan wakilcin yankin a shekarar 2027 mai zuwa.
Kadaura24 ta tuntubi Mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa domin Jin ta bakinsa Kan zargin da Jobe ya yi masa, Amma bai daga wayar da muka buga masa ba.