Matsalar Ruwan: Shugaban K/H Wudil ya ba da Umarnin gyara rijiyoyin burtsatse 100 a yankin

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Shugaban karamar hukumar wudil Hon. Abba Muhammad tukur Talban Makaman Kano ya ba da umarnin gyaran rijiyoyin burtsatse na tuka-tuka guda 100 a fadin karamar hukumar.

Hakan ya biyo bayan koke koken da al’ummar karamar hukumar wudil ke kan matsalar Ruwa, hakan tasa nan take Talban makama ya bada umarnin a kawu kayan gyara domin tunkarar wannan matsala, Kuma cikin ikon Allah kayan gyara sun iso, tuni an fara wannan aiki.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Hakan na kunshe ne cikin wata Sanarwa da mataimaki ga shugaban karamar hukumar wudil kan kafafen yada labarai Com. Abba Ashiru Utai ya aikowa Kadaura24.

Rikici: Dan Majalisar NNPP ya zargi Sanusi Bature da yi wa Gwamnan Kano zagon kasa

Ya ce matakin da Shugaban karamar hukumar zai taka muhimmiyar rawa wajen magance matsalar karancin ruwan sha da ake fama da ita a yankin.

Sanarwar ta ce Abba Muhammad Tukur ya ba da Umarnin a kammala aikin ba tare da bata lokaci ba, saboda tuni duk kayan da za a yi aikin da su sun Isa karamar hukumar ta Wudil.

InShot 20250309 102403344

” Babu shakka a wannan karo za mu kawo karshen matsalar ruwan sha, kuma bayan kammala gyaran wadancan rijiyoyin burtsatsen za mu fara gina wasu sabbin rijiyoyin .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...