Mijina bai yi sata ba kuma kudin da ya tara wa Nijeriya duk an wawashe su – Maryam Abacha

Date:

 

 

Maryam Abacha, matar marigayi Janar Sani Abacha, tsohon shugaban soja na Najeriya, ta ce mijinta ya ajiye wa Najeriya kudi, amma aka wawashe su bayan rasuwarsa.

A wata hira da aka yi da ita a gidan talabijin na TVC, wacce jaridar TheCable ta rawaito, Maryam ta bukaci a kawo hujja da ke nuna cewa mijinta ya boye kudaden sata a kasashen waje.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Abacha ya mulki Najeriya a matsayin shugaban soja da kuma kwamandan rundunar sojin kasa daga 1993 zuwa 1998, kafin rasuwarsa a ranar 8 ga Yuni, 1998.

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta kwato wasu kaso-kaso na kudaden da ake zargin Abacha ya boye a bankunan kasashen waje.

Rikici: Dan Majalisar NNPP ya zargi Sanusi Bature da yi wa Gwamnan Kano zagon kasa

A cewar rahotanni, daga shekarar 2020, an kwato sama da dala biliyan 3.624 daga cikin kudaden da Abacha ya boye.

“Wa ne shaida na kudaden da ake cewa an boye?” in ji Maryam.

“Ka ga hannu ko shaida cewa kudin na waje ne? Kuma kudin da mijina ya adana wa Najeriya, cikin ‘yan watanni sun bace. Babu wanda ke magana a kan hakan.”

InShot 20250309 102403344

Ta ce yadda ake ci gaba da zargin mijinta alamar wani mummunan hali ne da ke addabar al’umma.

“Me yasa kuke dora wa wani laifi? Ko kabilanci ne ko bambancin addini ne ko me ke damun ‘yan Najeriya?” in ji ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abun Alkhairin da mataimakin gwamnan Kano ya yi min ba a taba yin min shi a duniya ba – Kabiru D Bello

Tsohon Dan takarar shugaban karamar hukumar Gwarzo Alhaji Kabiru...

Gidajen Wasanni a Kano sun bi ka’idojin da muka sanya musu yayin bikin sallah – Abba El-Mustapah

Daga Rahama Umar Kwaru   A wani bangare na kokarin tabbatar...

Matsalar Ruwan: Shugaban K/H Wudil ya ba da Umarnin gyara rijiyoyin burtsatse 100 a yankin

Daga Rahama Umar Kwaru   Shugaban karamar hukumar wudil Hon. Abba...

Rikici: Dan Majalisar NNPP ya zargi Sanusi Bature da yi wa Gwamnan Kano zagon kasa

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Dan majalisar wakilai Mai wakiltar kananan...