Sarki Aminu Ado Bayero ya baiwa Alan Waka Sabuwar Sarauta a Masarautar Kano

Date:

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa

 

Mai martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji. Aminu Ado Bayero ya baiwa shahararren mawakin Nan Aminu Ladan Abubakar (Alan Waka) Sarautar Dan Amanar Kano.

Hakan na dauke ne cikin wani Sakon Sarkin da Sarkin Dawaki Babba Aminu Babba Danagundi ya fada , yayin bikin bajekolin wakokin Hausa na bikin sallah da aka gudanar a fadar Sarkin dake gidan Sarki na Nasarawa.

IMG 20250415 WA0003
Talla

” Mai martaba Sarkin Kano ya umarce ni da na fadawa Aminu Alan Waka cewa ya daga likkafar Sarautar da ya ba shi lokacin ya na matsayin Sarkin Bichi ta Dan Amanar Bichi zuwa Dan Amanar Kano”.

Soke Hawan Sallah: Dole Gwamnatin tarayya ta biya mu diyya – Gwamnatin Kano

Ya ce Sarkin ya ɗauki wannan matsayar ne bayan da ya Sami shawarwari daga manyan mutane a fadin Nigeria , don haka ya ɗauki shawarar kuma ya nada ka a matsayin Dan Amanar Kano.

InShot 20250309 102403344

Aminu Babba Danagundi ya ce za a saka lokacin da ya dace domin yin bikin nada Alan Waka a matsayin Dan Amanar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...