Daga Isa Ahmad Getso
Gwamnatin jihar Kano ta bukaci gwamnatin tarayya ta biya ta diyya bayan da aka soke Hawan Sallah na tsawon shekaru biyu a jere.
Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar, Alhaji Tajo Uthman ne ya yi wannan kiran a ranar Lahadi yayin da Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II ya kai wa Gwamna Abba Kabir Yusuf a gidan gwamnati.

Uthman ya ce jihar Kano ta tafka asara mai tarin yawa sakamakon soke hawan na al’ada wanda ake gudanarwa shekara-shekara wanda ya ke jawo hankalin masu yawon bude ido na cikin gida da waje.
“UNESCO ta amince da Hawan Sallar a matsayin bikin al’ada na gargajiya, wanda ake yi a lokacin bukukuwan sallah, Kano na samun makudan kudaden shiga daga kasashen waje saboda masu zuwa su kalli hawan daga ciki da wajen kasar nan,” in ji shi.
NiMet ta bayyana jihohin da za a sami tsawa da ruwan sama na kwanaki 3 a Nigeria
Kwamishinan Ya yi nuni da cewa, tasirin soke Hawan ya shafi tattalin arzikin kano wanda zai yi tasiri a kasafin kudin shekara mai zuwa na jihar.
Ya kuma jaddada cewa dole ne gwamnatin tarayya ta dauki alhakin Wannan asarar da ta jawowa jihar kano sakamakon soke Hawan don dale ne biya jihar diyya .
“Lokaci ya yi da za mu nemi a biya mu diyyar asarar da aka jawo mana,” in ji kwamishinan.
Uthman ya kuma yi kira da a gaggauta dawo da bukukuwan Hawan sallah a jihar Kano, yana mai bayyana sokewar a matsayin abin takaici.