Sallah: Kar ku bari a yi amfani da ku wajen tashin hankalin al’umma -Sakon Kungiyar ONE KANO AGENDA ga matasa

Date:

A yayin da al’ummar musulmi ke gudanar da bukukuwan Sallah babba, kungiyar One Kano agenda na mika sakonta na Barka da Sallah ga al’ummar jihar Kano da na kasa baki saya. Wannan lokaci ne na ibada da zaman lafiya, kuma lokaci ne na karfafa dankon zumunci da ke hada kan dukkanin al’umma.

Lokacin sallah ba wai lokaci ne kawai ba ibada ba, lokaci ne na nuna tausayi da hakuri, yafiya, biyayya da da’a ga Allah domin neman yardarsa mafi girma.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa Mai dauke da sa hannun Babban Daraktan kungiyar ONEN KANO AGENDA Amb. Abbas Abdullahi cissp,ipma, wadda ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.

A Wannan lokaci mai girma, kungiyar ONE KANO AGENDA ta yi kira ga daukacin al’ummar kasa, musamman ma matasa, da su rungumi zaman lafiya, hakuri, da hadin kai. “Ka da ku yarda a yi amfani da ku wajen ta da fitina a kano ta Kowacce fuska, domin Kano ta bunkasa ne da zaman lafiya da kaunar juna ba da tashin hankali ba.

Sallah: Baffa Babba ya raba buhu 2,000 na Shinkafa ga Kungiyoyin Tinubu a Kano

“Dole ne mu yi watsi da duk wani nau’i na rashin gaskiya kuma mu yi aiki tare don kare zaman lafiya, kwanciyar hankali, da kimar jiharmu ta Kano, mu amfani da Wannan lokaci na sallah wajen yin abubuwan da suka dace da za su kara darajar jiharmu mai albarka “. Inji sanarwar

Amb. Abbas Abdullahi ya kara da cewa “A matsayinmu na kungiya mai akidar Kano ta mu ce, muna kara jaddada aniyarmu ta tabbatar da adalci, hada kai, da kuma martabar kowane dan jihar kank. Mu hadu mu gina Kano inda ake daukar kowa da daraja, ake girmama mutunci da ra’ayin kowa.

InShot 20250309 102403344

Da fatan wannan Sallah za ta kawo mana waraka da hadin kan al’ummarmu, da albarka a kasarmu.

Daga Karshe Amb.Abbas Abdullahi ya taya daukacin al’ummar jihar Kano murnar sallah Babba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...