Zuwa ga: DG. Sunusi Bature Dawakin Tofa
Daraktan Yada Labarai,
Gwamnatin Jihar Kano
Ina rubuto wannan sakon ne cikin zafin rai da alhini mai zurfi, saboda irin abin kunyar da gwamnatin ku ta NNPP ke janyo wa al’ummar Jihar Kano a lokacin da ya kamata a nuna kulawa da tausayi. Lokacin Sallar Layya na karatowa, saura kwanaki biyu kacal, amma abin da gwamnatin ku ke rabawa mutane shi ne jakuna.
Ina tambaya da gaske: shin ana yanka jaki a Layya? A ina cikin addinin Musulunci aka ce jaki yana daga cikin dabbobin da ake yanka domin Layya? Akwai limamin addini da ya taba fadar hakan? Tabbas babu!

Wannan ba taimako ba ne, abin kunya ne.
Kano jiha ce mai tarin tarihi da daraja a idon duniya, jiha mai dogon alaka da addini da al’adu. Amma yau, ƙarƙashin jagorancin ku, an janyo wa wannan jiha abin dariya da rashin mutunci a idon al’umma. A daidai lokacin da mutane ke fama da tsadar rayuwa, farashin rago da saniya ya hau sama, kuna rabon dabbobin da ba su da alaka da ibadar da ake gab da yi.
Idan gwamnati zata taimaka da wani abu a irin wannan lokaci, kamata yayi ta fitar da raguna, shanu da kayan abinci, domin tallafa wa mabukata da mabiya jam’iyyar da suka sadaukar da lokaci da ƙoƙari wajen ganin jam’iyyar NNPP ta samu nasara.
Dama ba mu yi shirin yin hawan babbar Sallah ba – Sarki Aminu Ado Bayero ya fadi dalili
Shin rabon jaki shi ne sakamakon goyon bayan su?
Shin wannan shi ne sauyi da kuka ɗauka alkawari a lokacin kamfen? Ko kuwa kuna nufin ba ku san yadda ake tafiyar da mulki ba, sai ku koma abin ban dariya?
Dole ne mu fuskanci gaskiya: Wannan rabon jaki a lokacin Layya ya zubar da mutuncin gwamnatin ku kuma ya nuna rashin fahimtar lokuta da bukatun jama’a. A yanzu da ake bukatar jagoranci mai tausayi da fahimta, sai gwamnati ta koma rabon dabbobin da ba su da amfani ga bukatun mutane, ballantana a addini.
Ina kira gare ku da gaggawa: Dakatar da wannan rabon jakuna! Ku gyara wannan abin kunya kafin Sallah ta iso. Ku fitar da abubuwan da suka dace—raguna, shanu, kayan abinci—ku rabawa al’umma da kanku, ba tare da nuna bambanci ba. Ku dawo da mutunci da darajar da al’ummar Kano suka dade da ita.
Ina tabbatar muku: Wannan lokaci ne na Layya, ba na jakuna ba.
Tarihi zai rubuta wannan lamari. Al’umma zasu tuna. Kuma Allah zai tambaye ku.
Daga Faizu Alfindiki