Daga Nura Adam
Kansilan mazabar Lajawa a karamar hukumar Wudil ta jihar Kano Hon. Muttaka Lawan ya rabawa mutane sama da 100 a mazabarsa kimanin Kudi Naira dubu Dari Biyar domin su gudanar da shagulgulan sallah Babba.
Da yake jawabi a wajen taron Hon. Muttaka A Lawan ya ce ya raba kudaden ne domin al’ummarsa su sami damar gudanar da bukukuwan babbar Sallah cikin nutsuwa.

” Mun kawo wannan abun alkhairin ne a wannan lokaci da mu ka san cewa al’umma suna cikin wani hali, don haka muke fatan za ku yi hakuri da dan abun da mu ka samu har mu ka kawo muku”. Inji Hon. Muttaka Lawan
Dama ba mu yi shirin yin hawan babbar Sallah ba – Sarki Aminu Ado Bayero ya fadi dalili
Ya ce wannan somin tabi ne, nan gaba zai cigaba da yin duk mai yiwuwa don tabbatar da ganin al’ummar mazabar Lajawa sun cigaba da sharbar romon dimokaradiyya.
An dai raba kudaden ne ga rukunonin mutane daban-daban kamar haka :
1. NNPP OPTION A
2. NNPP OPTION B
3. SOCIAL MEDIA
4. 5000 FOR 25 PEOPLE
5. KUNGIYAR MATA
6. KUNGIYAR DATTIJAI
7. 2000 FOR 20 PEOPLE
8. SAURAN YAN JAM’IYYA
Wasu daga cikin wadanda su ka amfana da tallafin sun yabawa kansilan tare da yin kira ga sauran Kansilolin da masu mukaman Siyasa da su yi koyi da Hon. Muttaka A Lawan wajen taimakawa yan jam’iyya da sauran al’ummar garin.