Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I Jibrin, a ranar Talata, ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan ‘yan wasan Kano 22 da suka mutu a wani mummunan hatsarin mota a ranar Asabar.
Mummunan lamarin ya faru ne a ranar Asabar a garin Dakatsalle mai tazarar kilomita kadan daga birnin Kano, yayin da ‘yan wasan ke dawowa daga gasar wasannin motsa jiki na kasa (NSF) da aka kammala a jihar Ogun.

Sanata Barau ya samu halartar karamin ministan gidaje da raya birane Honarabul Yusuf Abdullahi Atta da manajan daraktan hukumar raya arewa maso yamma (NWDC) Farfesa Abdullahi Shehu Ma’aji da tsohon dan majalisar wakilai Hon Faruk Lawan da shugaban ma’aikatansa Farfesa Muhammad Ibn Abdullah da jiga-jigan jam’iyyar APC da malamai da ‘yan kasuwa da sauran su.