Sallah: Gwamnatin Kano za ta hukunta gidan wasan da ya bar masu shigar banza da shaye-shaye

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

A kokarin ta na yaki da rashin da’a tare tsaftace yadda gidan wasanni da masu kidan DJ zasu gudanar da shagalin bikin sallah a Jahar Kano, Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano karkashin jagorancin Abba El-mustapha ta bayyana shirinta na saka kafar wando daya da duk wani gidan wasa da dakunan taro ko masu kidan DJ da a ka samu da aikata yin rashin da’a a yayin gudanar da bikin sallah a Jahar Kano inda Hukumar kafa wani kwamiti ta musamman da zasu kewaya gidajen wasannin tare da dakunan taro a ranakun Babbar sallah karkashin kulawar Alh. lawan Hamisu Dan Hassan Daraktan dake lura da sashin fina-finai na Hukumar.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Kwamitin wanda aikinsa shine saka ido a kan dukkannin gidajen wasannin da dakunan taro a Jahar Kano hadi da masu kidan DJ zai tabbatar ba’a bawa masu shigar banza ko shaye – shaye damar shiga gidajen wasannin ba ko dakin taro haka kuma, Hukumar ta hana hada maza da mata a guri daya a yayin bikin na babbar sallar. Abba El-mustapha yace kwamitin zai rinka aiki ne a dare da rana ta cikin sirri tare da bayyane tun a rana daya ga babbar sallah har zuwa lokacin da za’a kammala bikin sallar domin cimma nasarar aikin da akasa a gaba.

Sallah: Hussari ya sauke kabakin arziki ga yan jam’iyyar APC na karamar hukumar Gwale

Abba El-mustapha na Kara yin gargadi da kakkausar murya ga masu gidajen wasanni da dakunan taro tare da masu sana’ar DJ dasu bi dokokin Hukumar sau da kafa domin gujewa fushin doka. A karshe ya yi kira da iyaye dasu cigaba da kula da tarbiyar ya’yansu tare da addu’ar Allah yasa ayi bikin na sallah lafiya a gama lafiya

InShot 20250309 102403344

*Sanarwa daga Abdullahi Sani Sulaiman amadadin lawan Hamisu Dan Hassan Daraktan lura da sashin fina-finai na fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano*

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yansanda sun Haramta Hawan Sallah a Kano

Daga Abdulmajid Habib   Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta haramta...

Sanata Barau ya kai ziyarar jaje ga iyalan ‘yan wasan da suka rasu, ya bayar da gudunmuwar N22m

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I Jibrin, a...

Hawan sallah : Sarki Sanusi ya umarci hakimai su shigo cikin birnin Kano

Majalisar Masarautar Kano ta fitar da wata takarda mai...

Yadda kamfanin ganyen shayi na Z&Y ke fuskantar matsin lamba daga TOP TEAA

Wani matashin ɗan kasuwa daga jihar Kano, mai suna...