Ban San Taulaci ba Sai da na Zama Sarkin Kano – Sarki Sanusi II

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II, ya ce sai da ya zama Sarkin Kano sannan ya san hakikanin talauci .

Sarki Sanusi ya bayyana haka yayin laccar da aka shirya gabanin bikin cikar tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi, shekaru 60 a Abuja, ranar Asabar.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Tsohon Gwamnan na CBN ya ce, “Da yawa daga cikin Manya a Najeriya ba su san mene ne talauci ba, a matsayina na masanin tattalin arziki, tsohon Gwamnan CBN, ina ganin adadin matalauta, Amma ban san hakikanin talaucin ba sai da na zama sarki.

Iftila:I: Gwamnatin Kano ta Aiyana Ranar Litinin a Matsayin Ranar Hutu
“Kuma ka je kauye ka ga ruwan da suke sha, da gidajen da suke rayuwa a ciki, da kuma irin ajujuwan da suke Karatu a ciki wadanda ko rufi ba su da shi”. Inji Sarki Sanusi.

InShot 20250309 102403344

Muna cikin matsalar da ya kamata mu gyara ta fa, saboda dukkanin mu Muna rayuwa a birane, su kuma talakawa sun rayuwa cikin mawuyacin hali da ya kamata mu Kai musu dauki don inganta rayuwarsu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...