Kotun ɗaukaka kara dake Abuja, ta rushe hukuncin babbar kotun tarayya ta Kano kan zaben kananan Hukumomi.
Tun da farko jam’iyyar APC da wasu mutane ne suka shigar da karar inda suka nemi a dakatar da zaɓen saboda zargin cewa shugaban hukumar zaben ɗan jam’iyyar NNPP.

Da yake karanta hukunci, mai sharia Oyewumi ya ce tun da farko babbar kotun tarayya bata da hurumin sauraron ƙara kan batun, bare har ta yi hukunci.
Saboda haka kotun ta amince da bukatar waɗanda suka daukaka kara wato bangaren gwamnatin Kano.