Gwamnatin Kano ta fara biyan tsofaffin kansilolin APC hakkokinsu

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da fara biyan kudaden tsofaffin kansilolin da suka yi lokacin tsohuwar gwamnatin APC da Kudi sama da Naira Biliyan 16.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da al’amuran cikin gida na jihar kano Com. Ibrahim Abdullahi waiya ya aikowa kadaura24.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya cika alƙawarin da ya ɗaukarwa tsofaffin kansilolin da sukai mulki a lokacin gwamnatin Ganduje, na fara biyan haƙƙokin su wanda yace Abdullahi Ganduje ya nuna halin ko in kula dasu lokacin da yake kan mulki.

Kwamishina Waiya ya ƙara da cewa rukunin kansilolin da suka fito daga ƙananan hukumomi 44 daga kuma mazaɓu 484 gaba ɗayan su zasu karɓi haƙƙokin nan ba jimawa ba.

A karan farko dai kansiloli 903 ne suka amfana da naira biliyan ɗaya da miliyan ɗari takwas ₦ 1.8. waɗanda sukai aiki daga shekarar daga 2014 zuwa 2017.

InShot 20250309 102403344

Sai kuma rukuni na biyu da yawansu yakai su yakai 1,198 waɗanda sukai mulki a shekarar 2018 zuwa 2020 kuma zasu karɓi biliyan biyar da miliyan ɗari shida ₦5,6.

Na ƙarshe da sukai a shekarun 2021 zuwa 2024 da yawan su yakai 1,371 da suka zamo kansiloli a wancan lokacin da zasu amfana da biliyan takwas da miliyan ɗari biyu ₦8,2 wanda jimilla yakai biliyan goma sha shida kamar Kamar yadda Sanarwar ta bayyana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...