Daga Kamal Umar
Babban jami’in Shirin bankin duniya mai kula da zaizayar kasa, madatsun ruwa da albarkatun noma wato Acreasal na jihar Yobe Shehu Alhaji Muhammed, ya ce rashin wadataccen abinci wato food security ga al’ummar najeriya shi ne kashin bayan matsalar tsaro, tabarbarewar tattalin arziki, da matsanancin halin da ‘yan kasar suke ciki.
Jami’in ya bayyana haka ne a wajen taron karrama muhimman mutane a kasar nan da lambobin yabo, wanda kungiyar Wazobia mai rajin tabbatar da Shugabancin na gari da sasanta rikici tsakanin kabilu ta shirya.

Shi ma Shugaban kungiyar gamayyar direbobin Najeriya GDN Sadik Abdullahi Jada wanda aka karrama shi saboda jagoranci abin koyi da kungiyar ta su take yi a fannin tuki ta hanyar wayar da kan direbobi da taimakon juna hadi da rungumar ‘ya’yan abokan aikin su wadanda suka hadu ajalin su ta sanadin tukin, ya ce lambar yabon da aka bashi zata yi masa kaimi wajen ci gaba da zage damtse akan kungiyar ta su ta hanyar fadada ayyukan ta.
Adullahi Ahmed Yola, shi ne mataimaki na 1 ga shugaban kungiyar ta gamayyar direbobin najeriya GDN, yayi kira ga abokan aikin su da su tabbatar suna gabatar da ayyukan su bisa kwarewa da bin dokoki domin tsira da mutunci da kaucewa fadawa matsala, tare da bukatar su da su tabbata suna shiga kungiyoyin tuki domin kara samun kariya.
Kungiyar kafafen yada labaran yanar gizo ta bukaci gwamnatin Kano ta gyara hanyoyin dake karkara
Wakilin Kadaura24 ya rawaito cewar taron karramawar wanda ya gudana a nan Kano, ya shaida yadda kungiyar ta karrama sama da mutane 40 daga sassa daban-daban na kasar nan.