Yadda Mijina ya sake ni bayan ya damfare ni – Mansura Isa

Date:

Fitacciyar jaruma a Masana’antar Kannywood, Masurah Isah ta tabbatar da mutuwar aurenta na biyu, wanda ta bayyana cewa ya zo mata a wani yanayi na ba-zata, kamar almara.

Mansurah ta ce ita aure ta yi na soyayya, domin a cewarta, “so makaho ne”, amma ashe mijin da wata manufar daban ya zo, ba aure na gaskiya ba.

Mansurah ta bayyana haka ne a shirin Mahangar Zamani na BBC Hausa, inda BBC ta tattauna da ita tare da tsohuwar jaruma a masana’antar, Fati Mohammad kan zargin matan Kannywood da rashin zaman aure.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Da take shimfiɗa, Fati Mohammad ta ce mutane ne suke musu gurguwar fahimta, domin “shi aure yana rai, kuma idan Allah ya kawo ƙarshensa, dole sai ya ƙare. Mutane da yawa aurensu yana mutuwa, amma saboda ba a sansu ba, sai ba za a ji ba,” in ji ta.

Ta ce yawanci ana auren matan Kannywood ne don sha’awa, “kuma kin san tunanin mata daban da na maza. Wani da an yi auren, da ya biya buƙatarsa sai ya sake ki. Ba za a yi tunanin shi ya sake ki ba, sai a ce kin ƙi zama saboda ‘ta saba da kuɗi’. Ai idan mai kuɗi ne, idan jin daɗi ne akwai kudin da jin daɗin, to me zai sa ta fito?” in ji Fati.

Don kwangila ya aure ni’

A watan Yunin shekarar 2024 ne aka ruwaito Mansurah Isa ta sake wani auren bayan rabuwarta da tsohon mijinta Sani Danja.

Mansurah Isah da Sani Danja sun rabu suna da ƴaƴa huɗu: Iman da Khalifa da Sultan da Sudais, lamarin da ya ja hankali matuƙa saboda yadda aka kasance ana kwatance da aurensu.

InShot 20250309 102403344

An yi ta yaɗa wani faifan bidiyo na auren na biyu na Mansurah, wada a ciki ake cewa ta yi aure, mijin ya biya sadakin naira miliyan ɗaya, auren da Mansurah ta ce shi ma yanzu sun rabu.

“Gaskiya matan Kannywood da yawa muna faɗawa cikin soyayya da sauri, ba ma gane masoyanmu na gaskiya ko maƙiyanmu, kamar yadda ƴan siyasa suke,” in ji ta a lokacin da take ƙarin bayani kan batun Fati Mohammad cewa suna amincewa da namiji ne idan ya nuna musu da gaske aure yake so.

Ta ce, sun haɗu da tsohon mijin nata ne a sanadiyar wani kawunta, “na samu wata kwangila a Legas, da na ga ba ni da wani a can sai na sai na neme shi ya riƙa kula min da aikin, amma ni ce a tsakiya duk abin da ake buƙata ni zan yi magana,” in ji ta, inda ta ƙara da cewa ashe shi yana da wata manufa ta zama uwa da makarɓiya a kwangilar.

Ta ce saboda haka ne “ya bijiro mani da soyayya. Lokaci ɗaya kawai ya ce a zo a yi aure, ni kuma na amince. Na ga duk abin da nake so na samu, ya ce in cigaba da fim ɗina da duk sauran harkokin da nake yi. Aka ɗaura aure da daddare, kawai da safe ya ce min zai tafi Legas.”

Ta ce da ya zo auren ya zo da takardar yarjejeniya, “cewa in saka hannu ni Mansurah na amince ya cigaba da jagorancin kwangilar nan ta biliyan huɗu saboda ya zama mijina, kuma tunda maza ne shi zai riƙa magana da su kai-tsaye.”

Manurah ta ce tun da ya fara magana da su, shi ke nan ya daina ɗaga wayarta, suma suka daina ɗaga wayarta.

“A taƙaice dai tun daga lokacin nan har ya sake ni, ban sake saka shi a idona ba,” in ji Mansurah.

A game da halin da ta shiga, ta ce, “da ya daina ɗaga waya, sai aka je Legas aka same shi, sai ya ce wallahi shi ya manta ya yi aure. Daga baya aka buƙace shi ya sake ni, da farko ya ƙi, amma da ya ga za a yaɗa shi, sai ya amince ya yi sakin,” in ji ta, inda ta ce ta amince da ƙaddara

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...