Tsohon dan takarar shugaban karamar hukumar Rano a tutar jam’iyyar APC Aliyu Harazimi Rano ya ce muddin ana son jam’iyyar APC ta cigaba da samun karbuwa a jihar Kano, ya zama wajibi masu ruwa da tsakin jam’iyyar a Kano da su dakatar da kungiyar da Mukhtar Unguwar gini ke jawa gora .
” Ita Wannan kungiya ta unguwar gini muna zarginta da yin abubuwan da suke raba kan yan jam’iyyar APC, a maimakon kungiyar ta mai da hankali wajen hada kan yan jam’iyyar da dinke duk wata baraka don mu sami nasara a zabe mai zuwa”.
Hon. Aliyu Harazimi Rano ya bayyana hakan ne yayin wata hira da yayi da Jaridar Kadaura24 a ranar lahadi.
Ya ce duk wata kungiya dake cikin jam’iyyar siyasa ana yin ta ne don hada kan yan jam’iyyar, “amma ita Wannan mun ga lamarinta ya banbanta da sauran don haka muka ga dacewar ankarar da masu ruwa tsakin jam’iyyar tun Kafin lokaci ya kure mana.
Yadda Mijina ya sake ni bayan ya damfare ni – Mansura Isa
Ya ce ba a shugabantar kungiya da girman kai da nunawa wasu ba su Isa ba, to wadannan abubuwan suke zargin unguwar gini na yi a shugabancin kungiyar da yake yi, wanda ya ce hakan ba zai haifarwa jam’iyyar APC ta jihar Kano da mai ido ba.

Aliyu Harazimi Rano ya kuma shawarci Malam Nasiru Ja’o’ji da yi baya-baya da unguwar gini saboda zai iya rarwatse masa jama’ar da yake da su.
” Ja’o’ji ka fara siyasa da farin jini amma matukar ka cigaba da damka al’amuran siyasa gidanka a hannun unguwar gini to ba makawa zai korar maka jama’a, ban ce kar ka yi mu’amala da shi ba, amma dai kar ka damka komai a hannunsa. Inji Harazimi Rano