Gwamnatin Kano ta dakatar da nuna tallan maganin Gargajiya a Fina-finai da yawo a tituna

Date:

A wani mataki na tabbatar da bin ka’idoji tare da inganta sana’ar masu sayar da maganin gargajiya a Kano tare da masana’antar Kannywood, Hukumar Tace Fina-finai Dab’i ta Jihar Kano karkashin jagorancin Alh Abba El-mustapha ta dakatar da duk wani nau’in tallace-tallacen maganin gargajiya a cikin fina-finai ko masu yawo a tituna da lasifika.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya aikowa Kadaura24.

Shugaban Hukumar, Abba El-Mustapha ne ya bayyana cewa yawancin tallace-tallacen da ake yi a tituna da lasifika ko kuma a cikin Fina-finan na karya dokokin Hukumar, wadanda ke bukatar a tace su kafin a fitar da su ga jama’a.

Abba El-Mustapha ya bayyana hakan ne a ofishinsa yayin wata ganawa ta musamman da manema labarai.

A saboda haka Hukumar na umartar duk masu tallan Maganin gargajiya a tituna da lasifika tare da cikin fina-finai da su miko tsarin tallace tallacen Maganinsu domin tantancewa tare da samun sahalewar Hukumar a cikin mako daya, tun daga Laraba 21 Ga Mayu, 2025, domin kaucewa daukar matakin doka.

El-Mustapha ya kuma yi kira ga dukkanin tashoshin talabijin tare da Hukumar Kula da kafafen yada Labarai ta Kasa (NBC) da su goyi bayan kokarin da hukumar ke yi dan tabbatar da a na bin dokar Hukumar domin inganta tarbiyya a tsakanin al’ummar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...