Daga Maryam Muhammad Ibrahim
A kokarinta na tabbatar da ana bin dokar tace fina-finai sauda kafa tare da kara dora masana’antar kannywood a kan saiti, Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano karkashin jagorancin Alh Abba El-mustapha ta dauki wani gagarun mataki domin tsaftace yadda ake sakin fina-finai barkatai ba tare da cika ka’idar da doka ta tanadar musu ba na kawo kowanne film gabanta a tantance shi kafin ya isa ga idanun al’umma.
Hakan ta sa hukumar ta dakatar da wasu Manyan Fina-finai har guda 22 daga sakasu a kafafen Internet ko gidan TV
Abba El-mustapha ne ya bayyana wannan mataki biyo bayan tattaunawa da manyan jami’an Hukumar tare da dogon nazari domin kawo karshen korafe korafen da Hukumar take yawan karba dan kara inganta aiyukan Hukumar tare da masana’antar kannywood.

Abdullahi Sani Sulaiman shi ne jami’in yada labaran Hukumar ya bayyana fina-finai da aka dakatar kamar haka:
1. Dakin Amarya
2. Mashahuri
3. Gidan Sarauta
4. Wasiyya
5. Tawakkaltu
6. Mijina
7. Wani Zamani
8. Labarina
9. Mallaka
10. Kudin Ruwa
11. Boka Ko Malam
12. Wa yasan Gobe
13. Rana Dubu
14. Manyan Mata
15. Fatake
16. Gwarwashi
17. Jamilun Jiddan
18. Shahadar Nabila
19. Dadin Kowa
20. Tabarma
21. Kishiyata
22. Rigar Aro
Ya kara da cewa doka ce ta baiwa Hukumar damar tace duk wani film tare da lura da aiyukan ‘yan masana’antar kannywood matsawar suna da rejista da Hukumar a ko ina suke, A saboda haka ana shawartar masu daukar nauyin wannan fina-finai da su tabbatar da sun bi wannan doka ta dakatarwa tare da tsayar da saka wannan fina-finai a gidajen TV ko kafar internet.
Haka kuma ana sanar da su cewa su miko fina-finansu ga Hukumar domin tantance su tare da basu shaidar inganci ta tacewa nanda sati daya mai zuwa wato daga LITININ, 19 ga watan MAYU, 2025 zuwa 25 ga MAYU, 2025 domin gujewa fushin doka.
A karshe Hukumar ta nemi hadinkan dukkannin gidajen TV da Hukumar dake lura da kafafen yada labarai ta Nijeriya wato NBC kan su cigaba da taimakawa Hukumarsa domin samun nasarar abinda ta saka a gaba da cigaban Jihar Kano da masana’antar kannywood.