Jam’iyyar NNPP ta nemi afuwar Shugaban kasa Bola Tinubu da kuma jam’iyya mai mulki ta APC dangane da wasu kalaman suka da dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi a kwanakin baya.
Jam’iyyar ta gargadi Kwankwaso da kada ya kara amfani da sunanta wajen sukar Shugaba Tinubu da jam’iyyar APC, tana mai cewa tsohon gwamnan jihar Kano an kore shi daga NNPP tuni.

A wata sanarwa da sakataren yada labarai na kasa na NNPP, Dakta Oginni Olaposi, ya fitar a ranar Lahadi a Legas, jam’iyyar ta nesanta kanta daga kalaman Kwankwaso, inda ta bayyana cewa an katse duk wata alaka tsakaninta da Kwankwaso da kuma kungiyar Kwankwasiyya da yake jagoranta.
Da Ɗumi-Ɗumi: Labarin da ake yadawa kan matsayar siyasa ta ba gaskiya ba ne – Kwankwaso
“Muna neman afuwa ga Shugaban kasa Bola Tinubu da dukan iyalan jam’iyyar APC, karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Ganduje, bisa cin mutunci da kalaman batanci da Kwankwaso ya furta,” in ji Olaposi.
“Kwankwaso ya daina bayyana kansa a matsayin dan jam’iyyar NNPP da kuma amfani da sunanta wajen kai hari ga jam’iyyar APC da fadar shugaban kasa,” in ji shi. “An kore shi tun tuni, kuma maimakon ya zargi wasu, ya duba kansa idan mabiyansa suna komawa APC.”