Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
Hukumar tace fina-finai da dab’i ta Jahar Kano a yau ta tsayar da matsaya kan bikin nan da ‘yan mata ke sanya kananun kaya tare da yin rawar nuna fitsara wato KAUYAWA DAY, in da ta haramta shi.
Haka kuma, Hukumar ta sanar da dakatar da dukkannin dakunan taro da gidajen Biki na musamman wato ‘Event Centers’ har zuwa lokacin da za’a cimma matsaya kan dokokin da aka dora musu domin kawo tsafta tare da tabbatar da ba’a sabawa ka’idar addini ba ko kuma cin mutuncin al’ada.

Shugaban Hukumar tace fina-finai Abba El-mustapha ne ya bayyana hakan a yau Asabar a yayin wata ganawa ta musamman da manema labarai jim kadan bayan wani taron gaggawa da Hukumar ta gabatar da manyan ma’aikatanta a kan al’amarin na bikin KAUYAWA DAY.
Cikin wata sanarwa da kakakin Hukumar, Abdullahi Sani Suleiman ya fitar, Abba El-mustapha ya ce wannan mataki ya zama dole la’akari da korafe korafen da Hukumar ke karba tare da jan hankali daga malamai tare da wasu masu fada a ji a fadin jahar Kano.
El-mustapha, ya bayyana cewa wannan matakin an dauke shine bisa ka’ida kasancewar doka ce ta bawa Hukumarsa damar daukar mataki kan duk wani mai kidan DJ, ko masu dakunan taro da gidajen bikin na musamman wato event centers tare da damar saka ido a duk wani biki da ake gudanarwa a fadin Jihar Kano matsawar za’a saka kida ko waka.
Inganta ilimi: Shugaban Karamar hukumar Ungoggo ya kaddamar da rabon kayan koyo da koyarwar
El-mustapha ya kara da cewa dangane da wannan mataki Hukumarsa ta shirya tsaf domin kara hada hannu da jami’an tsaro na farin kaya, ‘yan sanda, Hukumar Hisbah da kuma yan Vigilante wato ‘yan kato da gora tare da sauran dattawan unguwanni da kuma kungiyoyin matasa a Jahar Kano domin tabbatar da an kawo karshen wannan rashin ta ido da ke damun al’umma.
MATAKAI 6 NA HARAMTA BIKIN KAUYAWA DAY A FADIN JAHAR KANO*
1. Dakatar da duk wasu dakunan taro tare da gidajen Bikin na musamman wato event centers har sai an cimma matsaya kan sababbin dokokin Hukumar.
2. Hada hannu da manyan jami’an tsaro na gwamnati.
3. Hada hannu da jami’an yan Kato da gora wato Vigilante, da kuma Hukumar Hisbah
4. Hada hannu da dattawan unguwanni tare da kungiyoyin matasa.
5. Hada hannu da Kungiyar limamai tare da zauran malamai na Jahar Kano domin Jan hankalin iyaye da duk wani mai iya fada a ji.
6. Hada hannu da masu Unguwanni, Dagatai da Kuma Hakimai