Daga Shehu Usaini Getso
Shugaban karamar hukumar Ungoggo Alhaji Tijjani Amiru Bilyaminu ya kaddamar da rabon Kayayyakin Koyo Da koyo don bunkasa Ilimi a yankin
Shugaban karamar hukumar Ungogo, Alhaji Tijjani Amiru Bilyaminu ne ya jagoranci kaddamar da rabon kayayyakin koyo da koyarwa a cibiyar yada addinin musulunci da ke yankin.

Alhaji Tijjani Amiru Bilyaminu ya bayyana cewa an samar da kayayyakin ne domin tallafawa ci gaban karatun dalibai.
Ya kuma mika godiyarsa ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa jajircewarsa wajen aiwatar da duk abun da zai bunkasa ilimi a Kano.
Karyewar gada ya jefa dubban al’umma cikin mawuyacin hali a Rano, Sun nemi Agajin Gwamnan Kano
A nasu jawabin sakatariyar ilimi ta karamar hukumar Hajiya Hussaina Ibrahim da kansilan ilimi Abdullahi Wakili sun tabbatar da cewa makarantun yankin sun karbi kayayyakin koyo da koyarwa tare da kayan shakatawa na zamani.
A nasa jawabin shugaban kwamitin ilimi na karamar hukumar, Alhaji Sammani Muhammad Zango ya bukaci malamai da su yi amfani da kayan tare da ci gaba da aiki tukuru domin bunkasa ilimi.
A wata sanarwa da jami’in yada labaran yankin Salisu Kassim Yakasai ya aikowa Kadaura24, ya ce wasu daga cikin shugabannin makarantu a yankin, Malam Isa Amunu da Malama Binta, sun tabbatar da aniyarsu ta yin amfani da kayan koyarwa da aka tanada yadda ya kamata.