Daga Umar Ibrahim kyarana
Manoman dajin dansoshiya dake karamar hukumar Kiru a jihar Kano, sun koka da yadda jami’an tsaron Civil defense ke cin zarafinsu saboda sun je gonakin domin sharewa don fara shirin tunkarar damuwar bana dake tafe.
Wani Manomi mai suna Abdullahi Umar kwida ya zanta da jaridar Kadaura24, ya ce sun ya je gonarsu dake dajin dansoshiya domin ya shareta, kawai sai yan civil defense suka ce sun kama su, su ka kuma tafi da su wani gida inda achan su ka ce sun ci tararsu Naira dubu 300 amma daga bisani suka biya naira dubu 70-70 .

Ya ce sana’ar noma ita kadai suka iya kuma ita suke yi, amma yan civil defense na kokarin ta dole sai sun hana su yin noman da su ke yi a dajin duk da cewa Karamar hukumar kira ita ce ta ba su damar yin noma a dajin don hana batagari zama a cikin dajin.
Shi ma wani manomi mai suna Rabi’u Ibrahim Madaki ya shaidawa jaridar Kadaura24 cewa shi ma an kama shi ya na tsaka da share gonarsa, inda aka kai shi wancan gida kuma aka ce an ci tararsa Naira dubu 55, haka ya biya saboda ba yadda zai yi.
Gwamnatin Jihar Kano ta Kaddamar da Kwamitin Gyare-gyare a ma’aikatar Lafiya
“Muna kira ga gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da ya sanya ba ki kan wannan zaluncin da ake yi mana, saboda mun san shi ba ya goyan bayan zalunci”.Inji shi
Shi kuwa Muhammad Bello Dan daji cewa ya yi Naira dubu 20 yan civil defense din suka karba a wurinsa da sunan tara, saboda sun same shi yana share gonarsa dake dajin dansoshiya a karamar hukumar Kiru.
Manoman sun roki Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da ya kai musu dauki saboda cin zarafinsu da ake yi, da kuma yadda ake karbar kudade a hannun su ba bisa ka’ida ba.
Jaridar Kadaura24 ta tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar civil defense dake jihar Kano SC Ibrahim Abdullahi don jin shin rundunar ce ta ba da ikon a rika karbar wadancan kudade a hannun manoman Koko jami’an ne suke gaban kansu.
Ya shaida mana cewa ba su da masaniya kan wadancan kudin da ake zargin jami’ansu suna karba , amma ya ce za su bincika sannan su sanar da Kadaura24 sakamakon binciken da inda ya kammala.
Ku biyo mu za mu cigaba da bibiyar wannan lamari.