Matakai 3 da gwamnatin Kano ta dauka kan kafafen yada labarai a jihar

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Gwamnatin jihar Kano ta ce a kokarinta na magance matsalar cin zarafin al’umma da ake yi a kafafen yada labarai da sunan adawar siyasa ta dauki wasu kwarararan matakai har guda uku.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan aiyuka na musamman na ma’aikatar yaɗa labarai ta jihar Kano Sani Abba Yola ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Ya ce an amince da wadannan matakai ne a wani zaman na musamman da kwamishinan yada labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya gudanar da shugabannin kafafen yada labarai dake Kano.

Matakan guda uku su ne kamar haka:

Yadda manoma a Kano suka zargi jami’an Civil defense da karbar kudade a wajensu

1. Duk wanda ya zo zai yi hirar siyasa a gidan Radio to dole ne ya rubuta takardar alkawarin ba zai ci zarafin kowa ba, kuma na zai bata sunan kowa ba, haka kuma ba zai yi duk wani abu kawo hargitsi ba.

2. An haramtawa masu gabatar da shirye-shirye yin tambayoyin da za su tunzura wanda suke hira da shi, don gudun kada hakan ya dawo bata suna ko cin zarafin wani.

3. An haramtawa dukkanin kafafen yada labarai dake aiki a jihar yada Shirye-Shiryen Siyasa kai tsaye don gudun yin abubuwan da ba su dace ba.

InShot 20250309 102403344

Sanarwar ta ce dukkanin Shugabannin kafafen yada labaran sun amince da Wannan matakin tare da yin alkawarin tabbatar da shi a kafafen yada labaransu.

Hakan kuma kwamishina Waiya ya godewa Shugabannin kafafen yada labaran saboda hadin kai da goyon bayan da suke baiwa gwamnatin jihar Kano a koda yaushe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...

Rasuwar Buhari: Majalisar Nigeria ta dakatar da duk aiyukanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Majalisar dokokin Nigeria ta dage zamanta...

Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar...

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...