Ahmad Hamisu Gwale
Kungiyar Fulani ta FULDAN, ta bukaci gwamnatin tarayya ta fido da sabbin hanyoyin magance rikice-rikicen da ake samu a wasu yankun da Fulani da kuma makiyaya suke rayuwa.
A wani taron shugabannin kungiyar na shiyyar arewa maso yamma da aka gudanar a Kano a karshen mako, FULDAN ta ce magance matsalar zai kawo zaman lafiya.

Alhaji Muhammad Bello Dan Umma shugaban kungiyar na kasa, ya ce yanzu haka suna ta kokarin ganin an farfado da dangantakar dake tsakanin masu madafun iko wadanda suka fito daga cikin Fulani.
Ya kuma bukaci shugabannin kungiyar na jihohin arewa maso yamma, da su yi hobbasa wajen hada hannu da gwamnati domin samar da masahala ga makiyaya, tare da magance rikice-rikice a tsakanin su.
“Akwai bukatar a fahimci Fulani mutane ne masu son zaman lafiya, amma kowanne lokaci idan abu ya faru sai dora alhakin a kansu, wanda hakan rashin adalci ne”.
Gwamnatin mu ba wajen zaman Barayi ba ce – Gwamnan Kano Abba
Cikin wadanda suka gabatar da jawabai a taron akwai tsohon shugaban kungiyar na riko Alhaji Muhammad Dan Ali, wanda yace ilimantar da Fulani zai taka rawa wajen magance fadawar su cikin rikici.
Dan Ali ya kuma ce mafi yawancin wasu cikin shafaffu da mai ne a kasar nan, nada hannu a wasu rikice-rikicen da suke faruwa a sannan kasar nan.
Shima shugaban kungiyar FULDAN a Kano, Sani Adamu Dakata ya mika sakon godiyarsa ga wadanda suka halarci taron.
Taron shugabannin kungiyar FULDAN na shiyyar arewa maso yammacin Najeriya, ya samu halartar shugabannin yankin wadanda suka fito daga jihohin Kano, Jigawa, Katsina da Kebbi, sai Kaduna da zamfara da kuma Sokoto.