Daga Rahama Umar Kwaru
Tsohon Shugaban Rukunin Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), Mele Kolo Kyari ya bayyana cewa ya yi aikinsa da tsoron Allah.
Tun bayan babban sauyin da aka yi a kamfanin mai, rahotanni daban-daban sun fara yawo game da lokacin mulkin tsohon shugaban.

Daily Trust ta rawaito cewa wani rahoto ya nuna cewa an gano Naira biliyan 80 a asusun wani daga cikin daraktocin matatar mai da aka sauke, wanda ya yi aiki ƙarƙashin Kyari.
Zargin badakala: Ka fito ka fasa kwan, in ka ki mu fasa maka mugunya- Waiya ga Baffa Bichi
Bayo Ojulari, wanda ya gaji Kyari a matsayin shugaban rukunin kamfanin, ya fara babban sauyi wanda ya haifar da ficewar mutane da dama da suka yi aiki ƙarƙashin Kyari.
Haka kuma, an rawaito zarge-zargen cin hanci da rashawa daban-daban da su ka faru a lokacin da ya ke kan mulki.
Sai dai a yayin da ya ke mayar da martani kan wani rahoto da ya ce ya na hannun Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Kyari ya ce ya samu kiran waya daga mutane daban-daban dangane da labarin ƙarya.
Ya ce ya yi wa Najeriya hidima da tsoron Allah, kuma a shirye ya ke da ya bayar da cikakken bayani akan yadda ya gudanar da NNPC.