An karrama Sakatariyar NAWOJ ta Nigeria Wasila Ladan a Kasar Amuruka

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Wasilah Ibrahim Ladan, sakatariyar kungiyar mata ‘yan jarida ta kasa (NAWOJ) kuma babbar mai bayar da rahoto a gidan rediyon Najeriya, ta samu lambar yabo ta Kasa da kasa bisa jajircewarta wajen gudanar da aikinta.

Wannan babbar lambar yabo ana karrama yan jaridun da suka nuna kwazo da jajircewa da kuma sadaukar da kai wajen gabatar da aikinsu na aikewa da rahoto.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Gagarumin gudunmawar da Wasila Ladan ta bayar wajen inganta zamantakewar al’umma ta kafafen yada labarai da bayar da shawarwari kan ilimin ‘ya’ya mata, su ne su ka sanya har ta sami wannan lambar yabo a kasar Amuruka.

An yi la’akari da dabarun da ta ke amfani da su wajen Isar da sakonnin da suka shafi wayar da kan ya’ya mata.

Gwamna Yusuf ya taya Dangambo murnar zama shugaban kungiyar mawallafa labarai ta internet na Kano

Kyaftin Francis Asapokhai, shugaban kungiyar Prezens for Charity, da Misis Catherine Utsalo, mataimakiyar shugaban, sun bayyana jin dadinsu kan yadda Wasila Ladan ya samu gagarumar nasara a aikin jarida.

“Babu shakka ta sami wannan lambar yabon ne bisa chanchanta saboda yar jarida ce da ta nuna kwarewa wajen gudanar da aikinta”.

InShot 20250309 102403344

Ita ma a na ta jawabin bayan karbar lambar yabon Wasila Ladan, ta bayyana jin dadin ta, inda ta ce, “Na yi matukar Jin dadi da ba sami wannan babbar karramawar. Sannan ina godewa Kasar Amuruka da kungiyar da suka ba n wannan lambar yabo, haka zalika ina godewa ga Salma Yusuf shugaban sashin wasanni ta Freedom Radio
Kano, kuma Jami’in yada labarai ta
U20 Falconet.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Karin bayani game da shirye-shiryen Jana’izar Buhari

Gawar tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta baro birnin...

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...