Hukumar Shari’a ta Kano ta Gargadi Alkalai 2, ta kuma dakatar da Magatakarda 2

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Hukumar kula da shari’a ta jihar Kano ta dauki matakin ladabtarwa a kan wasu jami’an kotuna hudu, inda ta dakatar da wasu magatakarda biyu tare da yin gargadi ga alkalan kotun shari’a biyu bisa nuna rashin kwarewa da cin zarafin aikinsu.

Mai magana da yawun hukumar, Baba Jibo Ibrahim ne ya fitar da sanarwar daukar hukuncin ladabtarwar.

Ibrahim ya bayyana cewa, an cimma matsayar ne a yayin taron hukumar karo na 80 da aka gudanar a ranar 22 ga Afrilu, 2025, bisa ga shawarwarin kwamitin korafe-korafen jama’a na bangaren shari’a.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Daga cikin wadanda aka dakatar har da Ibrahim Adamu, babban magatakarda na biyu a babbar kotun shari’a, wanda aka dakatar da shi ba tare da biyansa albashi ba na tsawon watanni shida.

Har ila yau, an dage kara masa girma bayan da aka same shi da laifin zagi da kuma yunkurin kai wa nagaba da shi hari – wanda ya saba wa dokokin ma’aikatan jiharKano (2004) da kuma dokokin hukumar kula da harkokin shari’a.

Da dumi-dumi: Sarki Aminu ya nada sabon Galadiman Kano

A wata shari’ar kuma, Maigida Lawan, babban magatakarda na kotun daukaka kara ta Shari’a, an hukunta shi ne bisa laifin nema tare da kuma yunkurin biyan bukatun kansa ta hanyar da bata dace ba.

Hukumar ta rage masa girma daga mataki na 13 zuwa mataki na 12 sannan ta dakatar da shi ba tare da biyansa albashi ba na tsawon watanni shida, nan take

Har ila yau, Alkalin Kotun Shari’ar Musulunci, Alkali Mansur Ibrahim, ya samu gargadi a hukumance bayan da aka tabbatar da cewa ya yi kalaman batanci ga mai kara.

InShot 20250309 102403344

An kuma gargadi abokin aikin sa Alkali Nasiru Ahmad, biyo bayan nuna bangaranci a shari’ar da ya yi.

 

Hukumar ta sake jaddada matsayar ta na yaki da cin hanci da rashawa da rashin da’a, inda ta yi gargadin cewa, duk wani jami’in kotu da aka samu da aikata rashin da’a zai fuskanci hukuncin ritayar dole.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta dakatar da nuna tallan maganin Gargajiya a Fina-finai da yawo a tituna

A wani mataki na tabbatar da bin ka'idoji tare...

Da dumi-dumi: NNPP ta nemi afuwar Tinubu kan kalaman suka da ake zargin Kwankwaso ya yi masa

  Jam’iyyar NNPP ta nemi afuwar Shugaban kasa Bola Tinubu...

Gwamnatin Kano ta dakatar da Dadin kowa, Labarina, Jamilun jidda da wasu fina-finai 19

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   A kokarinta na tabbatar da ana...

2027: Hon Abdulmumin Jibrin Kofa ya bayyana Matsayarsa kan takarar gwamnan Kano

Daga Zakariya Adam Jigirya   Dan Majalisar tarayya mai wakiltar kananan...