Zainab Abdullahi wadda aka fi sani da Zainab Indomie ta kasance ɗaya daga cikin fitattun taurarin Kannywood da a baya suka yi shura ko fice a masana’antar.
A baya jarumar ta yi fice a Kannywood ne sakamakon yadda ta iya fitowa a matsayi daban-daban, ta ƙware wajen iya kwalliya, sannan yadda take jan muryarta kan ɗauki hankalin masu kallon fina-finan Hausa a wancan lokacin.

Tauraruwarta na tsaka da haskawa a Kannywood, sai kwatsam aka daina jin ɗuriyarta a masana’antar, lamarin da ya sa masoyanta suka riƙa tambayar inda ta shiga.
To sai dai a cikin Shirin Mahangar Zamani na BBC Hausa, jarumar ta bayyana dalilan da suka sa aka daina jinta, da kuma inda ta koma bayan hakan.
Sai wani ya matsa wani zai samu wuri’
A cewarta, ɗaya daga cikin dalilan da suka sa ta ɓace a masana’antar Kannywood shi ne, lokacin yin hakan ne ya zo.
Hajjin bana: Saudiyya ta fitar da jerin Harsuna 20 da za a fassara hudubar Arfat da su
”Hausawa na cewa sai wani ya matsa sannan wani ke samun wuri, idan wanda yake wuri ya ce shi ba zai matsa ba, to na bayansa ba za su taɓa samun wuri ba, su ma su kai inda ya kai”, a cewar Indomie.
”Idan mutum ya ci nasa to yana da kyau ya bai wa wasu dama su ci rabonsu”, a cewarta.
A shekarun baya an yi ta yaɗa raɗe-raɗin cewa ta haɗu da wasu gungun mutane da ake zargin cewa sun ɓata tarbiyyarta.
To sai dai jarumar ta musanta batun, tana mai cewa labarin ba shi da tushe.
Tana mai jaddada cewa lokacinta ne kawai ya yi a masana’antar shi ya sa aka daina jin ɗuriyarta.
Adam A Zango ne silar shigata fim’
Zainab Indomie ta ce Adam A Zango ne silar shigarta masana’antar Kannywood.
Ta ce tun tana ƙarama take da sha’awar harkar film, kodayake aikin jarida shi ne babban burinta.
Jarumar ta ce Allah ne sirrin ɗaukakarta a shekarun baya, da kuma yadda ta mayar da hankali kan sana’arta saboda yadda take son sana’ar a zuciyarta.
Indomie ta ce babu mutumin da ya taimaketa har ta kai matsayin da ta kai a masana’antar Kannywood kamar Adam A Zango.
”Adam A Zango ne ya kai ni masana’antar fim sannan ya haɗa ni da mutanen da suka sanya ni a fina-finai har na kai matsayin da na kai a masana’antar”, kamar yadda ta yi ƙarin haske.
‘Mun yi soyayya da Adam A Zango‘
Jarumar ta kuma tabbatar da cewa a baya ta yi soyayya da jarumi Adam A Zango, kuma ta yarda da halayensa.
”Tabbas mutumin kirki ne, kuma masoyine na ƙwarai, ya iya kula da budurwa”, kamar yadda ta bayyana.
Sai dai bayan sake dawowarta masana’antar a yanzu ana ganinta da tsohon zuman nata, lamarin da ya sa wasu ke ganin ko wataƙila ungulu ce za ta koma gidanta na tsamiya.
To amma Jarumar ta musanta wannan zargi, tana mai cewa ai duk abin da aka wuce shi a baya, to an wuce layinsa.
Ta kuma ce a yanzu haka tana da saurayi, kuma tana fatan yin aure nan da wani lokaci idan Allah ya yarda.
‘Babu wata ɗaukaka da ban samu ba a Kannywood‘
Jarumar ta ce a yanzu ba ta da burin cimma wani abu a masana’antar Kannywood.
”Duk wata ɗaukaka da ake samu a masana’antar Kannywood, babu wadda ban samu ba”.
”Duk wani mataki da jarumi zai kai a masana’antar sai da na kai, sai da sunana ya karaɗe wurare masu nisa, inda ban sani ba, don haka a yanzu ba ni da wani buri a Kannywood sai gamawa lafiya”.
Zainab Indomie ta ce babu wani abu da ya zame mata ƙalubale a lokacin da take kan ganiyarta a masana’antar.
”Ni ba mai saka damuwa ce a raina ba, don haka ko da wani abu ya dame ni zan yi ƙoƙarin hana ya ɓata min rai”, in ji ta.
Jarumar ta ce abin da ta sanya a gabanta shi za ta yi, babu ruwanta da kowa, don haka ne ma take rayuwarta ba tare da wasu matsaloli sun yi tasiri a rayuwarta ba.
”Abin da mutane ke tunanin zai ɓata min rai, ni ba shi ke ɓata min rai ba, idan na san wani zai yi wani abu don ya ɓata min rai, to hakan ba zai ɓata min rai ba”, in ji ta.
‘Abin da ba zan taɓa mantawa ba a rayuwata‘
Zainab Indomie ta ce abin farin cikin da ba za ta taɓa mantawa da shi ba a lokacin da take kan ganiyar fitowa a fina-finai, shi ne ranar da aka fara gane fuskarta a bainar jama’a.
”Ranar da na fita mutane suka gane fuskata, ita ce ranar da ba zan taɓa mantawa ba a rayuwata a Kannywood, na yi farin ciki marar misaltuwa”.
”Akwai wata makaranta a kusa da gidanmu, to ranar na fito daidai lokacin da aka taso yara daga makarantar, ai kuwa nan take suka fara kallona suna cewa ga wannan da muke gani a fim ɗin dawo-dawo”, kamar yadda ta bayyana.
Ta ƙara da cewa saboda murna a ranar sai da numfashinta ya fara ɗaukewa