Hukumar Hisbah ta kai samame tare da rushe wani tarin taɓo da aka ce an ga sawun Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama a wajen a jihar Kano.
Jaridar Leadership ta rawaito cewa wajen, a unguwar dakata, an share ne domin aikin layin dogo da zai bi ta wajen, amma sai mutane su ka maida shi wani waje mai tsarki na ibada saboda an ga idon ruwa ya na tsatsafowa a daidai wajen wani tarin ƙasa.

An ga wani faifen bidiyo da ya karade kafofin sadarwa, inda mutane ke ta tururuwa su na kallo, wasu kuma na yi wa mai tsarki da za su samu albarka da kuma tafiyar zunubai da samun waraka daga cututtuka tunda wai sawun Annabi ne a wajen.
Sai dai kuma tuni hukumar ta Hisbah, ta bakin Mataimakin Kwamandan hukumar, Malam Mujahideen Aminuddeen ya ce an rushe wajen kuma an kori mutane.
A cewar sa, shirme ne da kuma jahilci, duba da cewa Annabi Sallallahu alaihi Wasallama bai taba taka nahiyar Afrika ba.
Malam Mujahideen ya ce irin wannan ta’adar kan janyo Musulmi ya rasa imanin sa, inda ya yi kira ga masu aikata hakan su yi gaggawar tuba su kuma daina.