NAHCON ta sanar da ranar da za a fara jigilar Maniyatan Nigeria zuwa kasar Saudiyya

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Hukumar kula da aikin hajji ta Nigeria NAHCON tare da amincewar hukumomin jin dadin alhazai na jihohi sun amince da ranar 9 ga watan mayun shekara ta 2025 a matsayin ranar da za a fara jigilar Maniyata aikin hajjin bana daga Nigeria.

A wata sanarwa da mataimakiyar daraktan yada labarai ta hukumar NAHCON Fatima Sanda Usara ta fitar, ta ce an Amince da ranar ne a wani taro da sakatarorin hukumar jin dadin alhazai na jihohi .

IMG 20250415 WA0003
Talla

A jawabinsa shugaban hukumar NAHCON Farfesa Abdullah Saleh Usman ya tunatar da mahalarta taron cewa yanzu haka a matakin karfe ake na shirin gudanar da aikin hajjin bana.

Ya kuma yi kira ga Jihohin da su kara sabunta Hukumar NAHCON akan matakin da kowace jiha ta samu a fannin samar da Biza, allurar rigakafi, siyan jakunkuna da sauran su.

Hisbah ta rushe wajen da aka ce sawun Ma’aiki ya fito a jihar Kano

A yayin taron, kwamishinan ayyuka na hukumar NAHCON Prince Anofiu Elegushi ya bayyana cewa Air Peace zai dauki Maniyata 5,128 daga jihar Abia, Akwa Ibom, Anambra, Sojoji, Bayelsa, Benue, Borno, Cross River Delta, Ebonyi, Edo, Ekiti, Enugu, Imo, Kogi, Ondo, Rivers, Taraba da Taraba.

A daya bangaren kuma FlyNas tan ware masa maniyyata 12,506 da suka fito daga Babban Birnin Tarayya, (FCT Abuja), Kebbi, Lagos, Ogun, Osun, Sokoto da Zamfara domin kaisu kasa mai tsarki, kuma ya ce FlyNas zai kawo jiragen sama guda tara domin gudanar da aikin.

InShot 20250309 102403344

Kamfanin Max Air shi ne zai yi jigilar Maniyatan da suka fito daga jihohin Bauchi, Gombe, Jigawa, Kano, Katsina, Kwara, Oyo da Plateau. Kamfanin jirgin ya yi alkawarin zai kammala jigilar Maniyata 15,203 da aka ba shi a ranar 24 ga Mayu.

Kamfanin Umza kuma dai an ware masa mahajjata 10,163 da suka fito daga jihohin Kaduna, Adamawa, Nasarawa, Neja da Yobe.

An bayyana cewa akalla 43,000 ne za su sauke farali a bana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dalibai 22 sun kammala karatu da daraja ta 1 a bikin yaye ɗalibai na farko na Jami’ar Baba-Ahmed Kano

Jami’ar Baba-Ahmed, Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai...

Rundunar Sojin Amuruka ta kammala tsara yadda za ta kawo wa Nigeria hari

  Rundunar sojin Amurka da ke Afirka, AFRICOM, ta gabatar...

Kalaman Trump: Gwamnatin Nigeria ta Fara tattaunawa da Gwamnatin Amuruka

Gwamnatin Najeriya ta ce a gwamnantance tana tattaunawa da...

Ba zan bar Siyasa ba har lokacin da zan bar Duniya – Mal Shekarau

Tsohon Gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya ce...