Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Wata gobara da ta tashi a jihar Kano ta yi barna sosai, inda ta kone shaguna da wata makaranta mai zaman kanta da ke unguwar Rijiyar Zaki.
A cewar jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:53 na rana a ranar asabar 20 ga watan Afirilun 2025.

Ya ce hukumar ta samu kiran gaggawa daga wani mazaunin unguwar, mai suna Hamza Muhammad, inda ya sanar da su abin da ya faru a Rijiyar Zaki Kwanar Yan Kifi.
“Ma’aikatan kashe gobara daga hedkwatar hukumar, da kuma ofishin hukumar dake Rijiyar Zaki da Bompai, su ne suka kai dauki gaggawa domin kashe gobarar.
Gwamnatin Kano, za ta kula alakar Noma, kasuwanci da makamashi da kasar Morocco
“Da isar jami’an kashe gobarar sun gano wani bene na ci da wuta, inda aka ce wutar ta tashi ne daga wani shago da ake sayar da Gas , inda wutar ta kone Shagunan da wasu motoci biyu da ke kusa da wajen.”
Ya kara da cewa gobarar ta tashi ne a lokacin da ake sauke iskar gas daga wata mota kirar J5 a shagon.
Wutar ta kone ajujuwa bakwai da wani ofishi da bandakunan wata Makaranta mai zaman kanta mai suna Young Marshall Science Academy, dake kusa da inda gobarar ta tashi.
Ya ce gobarar ta kone shaguna uku, motoci biyu, da ajujuwa bakwai, sai kuma wata mota ta dan samu matsala.